Babban Darakta a ma’aikatar jin dadin Alhazai ta jihar Katsina Alhaji Suleman Nuhu kuki ya yaba da yanda alhazan na jihar Katsina suka nuna da’a a aikin hajjin ba, inda ya godewa Gwamnatin jihar Katsina, akan kokarin samar da masauki kusa da Harami. Sana yayi bayani sosai akan irin nasarorin da aka samu, na masaukai masu kyau da inganta ciyarwa da gudumawar da Gwamnatin jihar Katsina ta ba ko wane mahajjaci ta Riyal dari uku-uku (3)
Yace wannan nasara kacokam zamu alakantata ga Gwamnatin jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Aminu Bello Masari.
Source:
Katsina City News
Via:
Zaharadeen Mziag