Shugabancin Jam’iyyar PDP na ƙasa ya amince da tsawaita wa’adin lokacin sayar da fom ɗin tsayawa takara na jam’iyyar a kowanne mataki da mutum yake da sha’awar tsayawa a babban zaɓen 2023 .
Jam’iyar ta yanke wannan mataki ne biyo bayan hutun kwana biyu da gwabnatin tarayya ta bayar .
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyar, Debo Oluganagba ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce, an kuma sake canja ranar da za’a rufe karɓar fom ɗin bayan an cike da kuma ranar da za’a tantance ƴan majalisar jihohi da kuma majalisar ƙasa kamar haka:
A karkashin sabuwar ranar , za’a rufe saida fom zuwa ranar Talata, Afrilu 19, 2022, za’a rufe karbar fom ranar Laraba Afrilu 20, 2022
An zabi wadannan ranakun domin su zama ranar da za’a tantance dukkan yan takarkaru a kujeru ma banbanta ;
Ranar da za’a rufe karɓar fom ɗin da aka cike:
Ranar tantance ƴan takara :-
1 . Majalisar jiha: Juma’a – 22, ga Afrilu, 2022.
2. Majalisar tarayya :- Litinin 25 ga Afrilu, 2022.
Gwabnoni : Talata , Afirilu 26 ga Afrilu 2022
Shugaban kasa : Talata, 26 ga Afrilu 2022
Karbar korafi akan tantance yan takara
Majalissar jiha : Litinin, 25 ga AFrilu 2022
Majalissar Tarayya : Laraba 27 ga Afrilu 2022
Gwamna : Juma’a, 29 ga Afrilu, 2022
Shugaban kasa : Asabar , 30 ga Afrilu , 2022
Dukkan sauran ranakun da aka sanar a baya basu canza ba .
Sanarwar ta ce a kiyaye : kowanne fom na majalissar jiha za’a maidashi sakatareriyar jamiyya dake jihar ne ba helkwatar jam’iyyar dake Abuja ba.