Jam’iyyar PDP ta nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta kwace kujerar Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle saboda sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Karar, mai lamba: FHC / ABJ / CS / 489/2021, wasu mambobin PDP biyu ne daga jihar Zamfara – Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammed suka shigar da ita.

Masu shigar da karar suna kalubalantar cewa, saboda hukuncin da Kotun Koli ta yanke a baya, kan cewa APC ba ta da wani dan takara a zaben gwamna a 2019 a Jihar Zamfara, kasancewar ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba, to zai zama haramun ne ga Matawalle ya ci gaba da zama a ofishin sa a matsayin Gwamna a karkashin jam’iyyar APC, bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, kuma ya sauya nasarar PDP zuwa APC.

Suna son kotu ta bayyana cewa dole ne Matawalle ya yi murabus daga ofishinsa kafin sauya shekarsa don bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) damar gudanar da sabon zabe, cikin watanni uku, don PDP ta maye gurbinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here