PDP ta ƙasa tace; Bata dakatar Kwankwaso ba

Jam'iyyar adawa ta PDP matakinnkasa tace bata dakatar da Kwankwaso da Babangida Aliyu na Niger ba

PDP ta ce ba ta dakatar da Kwankwaso ba

@Twitter/Kwankwaso

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta musanta wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke cewa jam’iyyar ta dakatar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da takwaransa Babangida Aliyu na jihar Neja.

Cikin wata sanarwa da PDP ta fitar a shafinta na Twitter ta ce, akwai wasu ka’idoji da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada gabanin dakatar da duk wani mamba.

PDP ta ce ba za ta amince da irin wadannan karyace-karyacen ba, wadanda za su iya kawo hargitsi cikin jam’iyyar ko kuma su haifar da rikici tsakanin mambobinta.

Haka kuma ta musanta dakatar da tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu tana cewa duka bayanan da aka fitar na dakatar da shi basu da tyshe bare makama.

Others
Image caption: PDP ta ce ta ba san daga ina wannan takaradr ta samo asali ba

Jam’iyyar ta shawarci shugabanninta a jihohin Kano da Neja da su hada kai wuri guda su kuma yaki irin wadannan bayanan da za su iya kawo rabuwar kai, a lokacin da ‘yan Najeriya ke bukatar jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here