Obasanjo Ya Nemi A Yi Wa Tubabbun ‘Yan Bindiga Afuwa

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo da Fitaccen Malamin addinin Sheik Ahmed Gumi sun nemi gwamnatin Buhari ta yi wa tubabbun ‘yan bingida afuwa.

Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da Malamin addinin ya kai wa tsohon shugaban Najeriyan a gidansa da ke jihar Ogun.

Obasanjo ya ce, “Yan bindigar da suka shirya fita daga daji da kuma daina muggan laifuka, a yi musu ahuwa a gtara halayyarsu a koya musu ayyuka a basu jari ya zama suna da aikin yi”.

Wannan ne karon farko da aka ji Obasanjo na irin wadannan kalamai game da matsalar tsaro da ake ganin ta kusa mamaye yankuna da yawa a kasar.

Sai dai kuma ba wannan ne karon farko ba da Sheik Gumi ke neman a yi wa ‘yan bindigar ahuwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here