Injiniya Nura Khalil ya amince zaya tsaya takarar gwamnan katsina a jam iyyar NNPP mai alamar kayan Marmari.
Wani jigo a jam iyyar ya tabbatar ma da jaridun katsina city news cewa sati mai zuwa injiniya zai yanki fom na tsayawa takarar.
Munyi kokarin magana da injinya amma mun kasa, don wayoyin shi basa tafiya.
In har ya tsaya, wannan shine karo na hudu da injinyan ya tsaya takarar gwamna.biyu a jam iyyun Adawa.daya a jam iyyar PDP lokacin tana mulki sai kuma yanzu.
Nura Khalil ya fito daga shiyyar funtua, Dan siyasa ne ,mai basira da hikima.yana kuma da ilmi.
A nazarin mu na tarihin siyasar shi , babbar matsalar rashin dakewa komin tsanani komin wuya.
Zai taho gadan gadan da yaji wuta, sai ya fara sanyi sai kuma ka neme shi ka rasa.
Hamshakin dan kasuwa ne, na kasa da kasa.kuma masanin harkar gine gine .
@ www.katsinacitynews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here