A ci gaba da habaka bangaren aikin gona, musamman noman shinkafa, shirin da Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari take yi, hadin guiwa da wata Gidauniya mai zaman kanta dake Kasar Koriya na ci gaba da samun tagomashi.

Wannan shiri, ya maida hankali ne wajen koyar da dabarun noman shinkafar na zamani tare da samar da irin shuka da sauran kayan bukatun noman wanda suka hada da taki, magungunan kwari da makamantan su.

Ya zuwa yanzu, wannan Gidauniya mai suna SAEMAUL GLOBALIZATION FOUNDATION ta gyara azuzuwan koyon darussa, dakunan tarurruka, dakin cin abinci, ofisoshi, dakunan kwanan dalibai da kuma filayen noman gwaji duk a cikin cibiyar Songhai dake a Makera cikin karamar Dutsinma.

Haka kuma, sakamakon shigar su cikin aikin noman shinkafar, a yanzu manoman dake Makera da kuma na Raddawa ta karamar hukumar Matazu, suna samun Tan Shidda (6) na shinkafar a duk kadada (hectare) guda, a madadin Tan Daya da rabi da suke samu kafin shigowar wannan Gidauniya.

Har ila yau, wannan Gidauniya ta dauki nauyin tura mutane goma (10) kasar ta Koriya domin samun ilmi mai zurfi kan harkar noman shinkafar ta yadda za su rika koyarwa ida Allah Ya maido su gida.

Bukatar da suka gabatar wa Gwamnati ta a basu damar amfani da filin da ya kai kadada Dari (100) wanda yake makwabtaka da wadannan garuruwa guda biyu domin fadada noman shinkafar, tasa Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyara wannan cibiya ta Songhai domin gane ma idon shi irin ayyukan da sukayi na raya wurin tare da irin yadda suke koya wadannan dabarun noma na shinkafa. Haka kuma Ya duba tare da yin nazari a kan wannan bukata tasu.

Babban Daraktan wannan Gidauniya mai kula da Najeriya Mista Kyungbok Lee ya zagaya da Gwamnan tare da yi mashi bayani kan ayyukan da sukayi dama wadanda suke son yi a wannan Cibiya.

A jawabin shi na gabatarwa, Babban Daraktan hukumar zuba jari ta jiha (Katsina Investment Promotion Agency) Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi, ya shaida wa Gwamnan cewa wannan Gidauniya tayi nisa wajen koyawa manoman wannan yanki dubarun noman shinkafa na zamani wanda hakan yasa aka sami rurrubawar yabanyar da suke samu a gonakin nasu.

Shi kuwa Babban Mai-Safiyo na jiha Alhaji Yunusa Lawal ya gabatarwa wa Gwamna Aminu Masari taswirar wuraren da wannan aiki ya shafa, musamman kadada Dari da wannan Gidauniya ta nema, a inda Gwamnan ya bada umurnin da a tabbatar da ba a taba filayen al’ummar wannan yanki ba, tare kuma da tsare masu duk hakkokin su a matsayin su na masu masaukin wannan Gidauniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here