NNPC ya zama kamfani mafi girman hannun jari a Najeriya

Buhari

Hukumar kula da harkokin kasuwanci a Najeriya ta Corporate Affairs Commission (CAC), ta ce kamfanin man fetur na ƙasar, NNPC, ya kafa tarihi yayin da hannun jarinsa ya zarce na kowane kamfani a Najeriya.

Rajistira na hukumar CAC Alhaji Garba Abubakar ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake gabatar wa Shugaba Buhari rajistar sauya fasalin kamfanin a fadar shugaban ƙasa ranar Juma’a.

Ya ce an yi wa kamfanin rajista cikin kwana ɗaya ta intanet da darajar hannun jarinsa a tashin farko ta kai naira biliyan 200 tun ranar 22 ga watan Satumba.

Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito Shugaba Buhari na bayyana jin daɗinsa game da nasarar da NNPC ɗin ya samu.

A watan Agusta ne Buhari ya sanya wa dokar Petroleum Industry Bill (PIA) hannu, wadda ta tanadi sauya wa NNPC fasali, ciki har da rusa shi zuwa na ‘yan kasuwa – maimakon na gwamnati kaɗai – cikin wata shida.

Social embed from facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here