NNPC: Kamfanin mai na Najeriya ba zai saka kudi a asusun gwamnati ba a watanni masu zuwa

Man Fetur

Rahotanni sun ambato kamfanin mai na Najeriya NNPC na cewa ba zai iya sanya ko sisin kwabo ba a asusun tarayya a watan Mayu mai zuwa.

Kamfanin ya ce hakan ya zama wajibi ne saboda gibin da ya samu a kudaden shiga Naira biliyan dari daya da goma sha daya (N111bn) a watan Fabrairun da ya gabata.

Ya kuma kara da cewa, ga kuma yawan kudaden da yake kashewa wajen bayar da tallafi ko rangwamen farashin man fetur a kasar.

Wata majiya a kamfanin na NNPC ta tabbatar wa da BBC cewa lallai kamfanin ya rubuta wasika ga kamfanin babban akanta na Najeriya yana shaida masa halin da ake ciki.

Majiyar ta kuma ce a duk wata, kamfanin kan kashe Naira biliyan dari daya wajen biyan kudaden tallafin mai da nufin saukaka farashin albarkatun man fetur da jama’ar kasar ke amfani da su.

NNPC din dai na nuni da cewa wannan yanayi ya sanya shi cikin tsaka mai wuya, da idan ya cigaba da bayar da gudumawa ga asusun tarayya, ba zai iya biyan tallafin mai ba, lamarin da ka iya sa farashin man ya yi tashin gwauron zabi a kasar da kuma kara tsadar rayuwa ga talakawan kasar.

A bangare guda kuma idan ya biya tallafin ba zai iya saka kudi ga asusun tarayya ba kuma shine matakin da ya dauka a yanzu.

Sai dai kuma wannan shi ma rashin bayar da gudumawa ga baitulamlin zai iya yin illa ga kudaden shiga na gwamnatoci a matakan tarayya, da jihohi, da kuma kananan hukumomi, abinda wasu ke ganin ka iya shafar gudanar da ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata.

BBC

Ya masana ke kallon lamarin?

Dakta Muhammad Shamsudden, malami a sashen nazarin tattalin arziki a Jami’ar Bayero dake Kano ya ce akwai ayar tambaya ga ikrarin na kamfanin mai na kasa.

“Ai abubuwan dubawa guda biyu ne shi wannan ikirarin da kamfani na NNPC ke yi shin gaskiya ne ko kuwa akwai alkaluma da suka nuna sabanin haka?” in ji masanin.

Ya kuma ce shi bai ga yadda za a iya biyan tallafin mai na biliyan dari da goma sha daya a wata daya ba musamman idan aka duba abubuwan da suka faru a baya.

“Misali a shekarar 2019 gaba daya tallafin man da Najeriyar ta biya kamar yadda shi kamfanin NNPC ya fitar da alkaluma, biliyan dari bakwai da hamsin da biyu a shekara guda”.

“Wannan ya nuna duk wata daya bai wuce biliyan sittin da uku ba amma sai yanzu ga shi suna maganar kashe biliyan dari da goma sha daya.”

“Baya ga haka ko da gaske ne ana biyan wannan tallafi amma ai man fetur din ya tashi a kasuwar duniya,” a cewar Dakta Shamsudden.

Masanin ya kuma bayyana cewa kasar ta yi kasafin kudi na man fetur kan dala 40 kan ko wace ganga a Najeriya, amma a yau yadda ake sayar da danyen mai ya kai dala 68 kan ko wace ganga- karin kashi 70 cikin dari na abinda Najeriya ta kasafta kenan.

“To idan haka ne menene zai hana a biya wannan tallafi biliyan dari da goma sha daya a wancan karin da aka samu?”, in ji shi.

Masanin ya kuma ce misali idan ma NNPC din ya gaza biyan abinda ya saba biya a asusun tarayya da ake rabawa, ya ce abinda ya gani a watan Maris an raba kudi dala biliyan dari shida da tamanin da daya a Najeriya, kuma a ciki abinda NNPC ya bayar bai wuce naira miliyan sittin da hudu ba, wanda bai kai ko kashi goma cikin dari na abinda gwamnatocin kasar suka raba ba.

Shamsudden ya ce gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi mafi yawancin kudin da ake ba su yana zuwa ne daga haraji.

Ya kuma kara jaddada cewa “Kudaden shiga da ke zuwa daga kasashen waje su ne mafi yawa da ke zuwa daga man fetur, amma mafi yawan abinda ake rabawa a gwamnatance na daga harajin cikin kasa da kuma wanda ake dauka daga asusun ajiyar rarar man fetur, amma shi ne mafi yawan abinda ake rabawa a cikin kasa”.

“Wannan magana ce ta yin ban-tsoro don ya nuna lallai sai ya cire tallafin mai, don haka ya ke korarin cewa tallafin mai ya hana shi bai wa gwamnatin kasa kudi,” in ji dakta Shamsudden.

Short presentational grey line

Najeriya na daga cikin kasashen da ke kan gaba a duniya wajen arzikin mai, kuma kasa ce da arzikin ta ya dogara kacokan kan kudaden shiga daga man fetur.

Kan haka ne tattalin arzikin ya gigita a sakamakon mummunan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya wanda annobar korona ta haddasa.

A bangare guda kuma, kasar ba ta da managartan matatun man fetur, wanda ya tilasta mata sayar da danyen man ta a kasashen waje, kana ta sayo tatattun albarkantun man domin amfanin jama’a a cikin kasar.

A wannan tsari mai rauni ne kuma kasar ke biyan kudaden tallafin mai domin saukaka farashin man a gidajen mai a kasar.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun sha kokawa kan cewa wannan tsarin na cike da almundahana ta yadda ‘yan kasar ke cewa sun kasa fahimtar yadda ake tafiyar da tsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here