Shugaban Kasa Buhari ya bayyana cewa ba zai yiwu ya saki shugaban kungiyar IPOB ba, Nnamdi Kanu wanda yake hannun jami’an tsaro tunda suka kamo shi daga kasar Kenya, bayan da ake ta mika mishi bukatar ya saki shugaban ‘yan awaren Biyafaran. Wannan ya biyo bayan ziyarar da dattawan kabilar Igbo suka kaiwa shugaban kasar, inda suka mishi bukatar sakin Kanu din.

Shugaban ya bayyana hakan ne a hirar da gidan Talbijin din Channels suka yi da shi da yammacin yau Laraba, inda suka yi mashi tambayoyi akan batutuwan da suka shafi kasa, musamman ma dai abinda ya shafi tsaron kasa.

“Batun Kanu yana gaban kotu, wanda bai kamata na tsoma baki ba. Amma abinda ya bani mamaki shine, lokacin Kanu yake Turai, ya dinga maganganun banza ga gwamnatinmu, ya dinga rashin kunya, a ganina tunda yanzu ya gurfana a gaban kotu yakamata ya iya kare kanshi a gaban doka.” inji Buhari.

Buhari ya kara da cewa, yanzu mun bashi damar ya kare kanshi ne, ba wai kawai ya buya a kasashen turai yana ta zaginmu ba, ba irin kalar cin zarafi da bai yi wa gwamnatinmu ba, yadda ka san ba dan Nijeriya bane shi, don haka mun bashi dama ya cigaba da zaginmu. Wadanda suka bukaci in sa baki a sake shi, yakamata su san bana yi wa kotu katsalanda, tunda maganar na gaban kotu, toh a kyale kotu ta yi aikinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here