Hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya (NIMET) ta yi hasashen za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu sassan kasar daga ranar Talata zuwa Alhamis.

Hukumar ta ce lamarin ka iya kawo tsaiko kan yadda ake tafiyar da zirga -zirgar jiragen sama cikin sauki a fadin kasar.

NiMET ta ce a cikin kwanaki uku masu zuwa, za a yi ruwan sama sosai a Kudancin Kebbi, Yammacin Neja, Katsina ta Arewa, Kano ta Gabas, Jigawa, Bauchi, Yammacin Yobe, Gombe, Kaduna, Filato, Nasarawa, Abuja ta Gabas da Jihar Kwara.

Hasashen yana kunshe ne a cikin Hasashen Yanayi da aka fitar a ranar Litinin.

NiMet ta ce akwai yiwuwar samun ruwan sama matsakaici a Cross River, Akwa Ibom, Benue, Ebonyi, Sokoto, Ekiti, Edo, Kogi, Ogun, Osun, Oyo, Enugu, Anambra, Imo, Abia, Ondo, Lagos, Delta da Bayelsa.

Duk da haka, ana sa ran samun ruwan sama a sauran sassan kasar, in ji hasashen.

A yankin da ake hasashen ruwan sama zai yi yawa, hukumar ta ce “Akwai karin yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a kan hanyoyi, matsugunai, gonakai da gadoji wadanda za su iya kawo tsaikon zirga -zirgar ababen hawa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here