Home Sashen Hausa Nijar: Adadin ƙabilu masu rinjaye na ƙasar- bbc

Nijar: Adadin ƙabilu masu rinjaye na ƙasar- bbc

Nijar: Adadin ƙabilu masu rinjaye na ƙasar

...

Kasar na a yankin Hamadar Sahara a Yammacin Afrika da kuma ke da tarihi mai yawa da al’adu daban-daban.

Al’ummar kasar na da manyan kabilu 10 da yawansu ya kai milyan 20, da ke da addinai daban daban.

Jamhuriyar Nijar kamar sauren kasashen Afrika, ta samu ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka a ranar uku ga watan Agusta na shekara ta 1960, daga Turawan Faransa.

A yau kasar na da al’ummar da yawanta ya kai milyan kimanin 20 da kuma ta kunshi manyan kabilu na kasar guda 10.

Kabilun Jumhuriyar Nijar sun hada da :

1-Hausawa

2 -Zabarmawa

3-Fulani

4-Azbinawa

5-Kanuri

6- Tubawa

7-Gurmawa

8-Buduma

9-larabawa

10-Tigidal.

Bayan wadannan kabilu guda 10 manya-manya na kasar da ke magana da harsunan su na asali, harshen Faransanci ya kasance harshe na 11 da ake amfani da shi a cikin kasar wajen tafiyar da harkokin yau da kullun na rayuwa a gwamnatance da kuma a makarantun boko.

A takaice shi ne harshen da aka fi anfani da shi a alkarya.

Al’ummomin kasar ta Nijar sun kunshi Musulmi da Kiristoci da masu addinin gargajiya da ma wadanda ba su da wani addini.

To sai dai kashi sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummar kasar Musulmai ne.

Nijar na da jahohi takwas da suka hada da Agadez da Zinder(Damagaram) da Maradi(Katsinar Maradi) da Diffa da Dosso da Tillabery da Tahoua(Tawa) da kuma babban birninn kasar Niamey(Yamai).

Garin Zinder wato Damagaram, shi ne babban birnin kasar na farko kafin a maidashi Yamai a ranar 26 ga watan 6 na shekara ta 1926.

Garin Maradi shi ne babban birin kasuwanci na kasar tun fil azal, kuma a nan ne aka kafa bankin farko a cikin kasar.

Nijar ta kasance kasa mai dumbin tarihi da al’adu daban-daban. Ta samo sunanta ne daga Kalmar ” NGARR ” daga wani harshe da ake kira ” BERBER.”

Kogin Kwara wato Issa Babban Gulbi ko kuma Fleuve NIger shima ya samo sunan shi ne ta hakan.

Kogin na Kwara na da tsawon kilomita 4,500 daga Guinea zuwa Najeriya, ya ratsa kasar ta Nijar da tsawon kilomita 550.

Duk da kansancewar kasar a tsakiyar Hamadar Sahara, a yankin Yammacin Afrika, Nijar na tunkaho da noma da kiwo wajen bunkasa tattalin arzikin ta.

Kasar na da kamfanoni da dama a baya da suka hada da SONARA da SOTRAMIL da SICONIGER da dai saurensu, waɗanda yanzu suka kasance sai suna kawai ya rage.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An yanke wa ‘yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana

An yanke wa 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana ‘Yan Najeriya biyu za su fuskanci da hukuncin kisa ta hanyar rataya a ƙasar Ghana...

Darakta Ashiru na goma ya warke daga ciwon da ke damun sa bayan likitoci sun tabbatar da hakan

Fitaccen darakta a masana'antar shirya fina finan Hausa ta KANNYWOOD Ashiru Na goma ya fito daga Abisiti, bayan Likitoci sun tabbatar da cewa yasamu...

Gwamnatin Kano ta Dakatar da muƙaba da Sheikh Abduljabbar

Yanzu-Yanzu: Wata kotun majistari da ke Gidan Murtala a Kano ta dakatar da gudanar da muqabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da sauran malamai, kuma...

Restoring Sanity at Nigerian Ports with Electronic Call-up System

Restoring Sanity at Nigerian Ports with Electronic Call-up System By Danjuma katsina Since July 2016, the Nigerian Ports Authority (NPA) under the leadership of Hadiza Bala...

Ma’aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya

Ma'aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci ma'aikata a mataki na 12 zuwa ƙasa da...
%d bloggers like this: