Shahrarren Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya sake kira ga gwamnatin tarayya cewa ta rungumi sulhu da yan bindiga saboda yaki ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba.

Sheikh Gumi ya ce al’ummar jihar Zamfara da ake artabu yanzu da yan bindiga kawai ke shan wahala saboda tuni yan bindigan sun gudu, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook, da Blueink News Hausa ta bibiya.

Ya ce yan bindigan yanzu sun fara shiga garuruwan da ko hanya ba su sani ba, amma duk da haka suna ci gaba da aikata laifin garkuwa da mutane saboda haka korarsu daga Zamfara ba zai yi amfani ba.

Gumi ya ce shi Malami addini ne mai digri 3, shi Likita ne kuma tsohon Soja; saboda haka don soyayyar kasa da al’umma yake abubuwan da ya ke yi.

Me Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Ga Sheikh Ahmad Gumi?

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya kalubalanci fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, kan cewa da ya yi farmakin da sojoji ke kaiwa zai kara munana ta’addanci a Najeriya.

Adesina a cikin wani wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba ya bayyana Gumi a matsayin “mai son yan fashi da makami ”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here