Advert
Home Sashen Hausa "Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku,...

“Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku, Kuji tsoron Allah”…..Saƙon Ɗan takarar Gwamna, Sanata Sadiq Yar’Adua ga Delegate.

“Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku, Kuji tsoron Allah”…..Saƙon Ɗan takarar Gwamna, Sanata Sadiq Yar’Adua ga Delegate.

 

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @ Katsina City News

Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua, Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, ya zagaya ƙananan Hukumomi 34 na jihar Katsina Domin Nasiha, jan hankali, Nuni da Tunatarwa, akan Masu zaɓen ‘Yan takara wato Delegate.

Sanatan ya shiga Shiyyar Daura, Funtua, Katsina, da Malumfashi, inda duk inda yaje. Yana ganawa da Ciyamomin Mulki, Kansiloli, Shuwagabannin Jam’iyya, da Masu Zaɓen Fidda Gwani Wato (Delegate).

“Ittaqillah! Ittaqillah!! Ittaqillah!!! Damu daku Duka muji tsoron Allah, bama kamar ku Delegate, Idan ƙasar nan da jihar mu, ta gyaru ku kuka gyarata, Idan kuma a ka sake komawa cikin wani bala’in da tashin hankali kune”  Sadiq Yar’Adua ya faɗa.

Ya tunatar da hadisin Manzon Allah (S) cewa; “Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana fadi a cikin hadisi, (Idan kaga ɓarna ko wani abinda ba daidai ba, to ka yaƙi abin (ka hana) Da ƙarfin ka, ko da Dukiyar ka, Ko da Ilimin ka, ko ka ƙyamaci Abin, Amma shine mafi raunin Imani”  Sadiq ya ƙara da cewa, “kowa yasan ƙasar nan ana Zalunci, jihar nan ana Zalunci, ni kuma nafito inyi yaƙi da Zaluncin, amma bani iya hana Zaluncin da ƙarfi, Saboda madafun iko basa hannun mu, sana kuma bana so inzama mai raunin Imani, tunda Allah ya bani Sukuni, na faɗa da Zaluncin da Dukiya domin cika Umarnin Allah da Manzonsa.” Injishi

Yace “To amma ku sani Zaluncin da ake a yanzu baka iya maganinsa da Dukiya, amma zaka iya maganinsa sa da ƙarfi, idan Allah ya baka Gwamnati, kuma ku Delegate kune zaku kama a samu Gwamnatin, har a yaƙi zaluncin da karfi.

Don haka nazo ku kama mani’in yaƙi Zalunci, kuma wannan, idan kuma baku kama aka yaki zalunci ba, ni dai har ga Allah na fita Saboda, Allah ya bani Damar da zan iya amfani da ita ta hannun ku, kune baku bani ba, ina fatan wannan ya isheni uzuri wajen Allah, saura dami…? Mala’iku zasu tambaye ku, da wane yazo yace yana so ku taimaka ayi fada da zalunci, mi yasa baku dafa mashi ba..?”  Sadiq ya tsoratar.

Yar’Adua ya kwarmata masu cewa akwai masu so suyi amfani da kuɗi su sayi ra’ayinsu ta hanyar basu Babura da a Dai-daita sahu, don su zaɓesu, Yace suji tsoron Allah kada a son Duniya yasa su jefa Rayuwar miliyoyin mutane cikin tashin hankali wanda kuma sune sila.

A ƙarshe yaja Kunne da gargaɗin Alhajin Birni da ake zargin zai sayi ‘yancin mutane da kuɗi da babura don su zaɓi ɗan takarar sa, inda yace, yaji tsoron Allah ya koma ga sana’arsa ya bar ‘Yansiyasa suyi tasu sana’ar.

Taron wanda aka gudanar a kowace ƙaramar Hukuma ɗaya da tazamo tsakiya, sai a haɗa a haɗa kananan hukumomi da ke kusa da ita a haɗu, domin sauƙaƙa Zirga-zirga. A ƙarshe dai kwalliya tana biyan kuɗin sabulu, kamar yanda makusantan Sadiq Yar’Adua suke faɗa cewa, lallai Nasiha ta shige su, sai dai mafatan kaɗa Sheɗan ya shigesu daga bisani.

Wakilin jaridar Katsina City News ya leƙa lungu da saƙo na inda Sanatan ya shiga kuma ya ganowa idanun sa.

Akwai Video zamu tace kuma mu sakar maku a Tashar mu, da Shafin mu, na Facebook domin ji da gani.

www.katsinacitynews.com

www.taskarlabarai.com

www.thelinksnews.com

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje….. Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina.

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje..... Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina. Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina...

Yunƙurin Ficewar Sanatoci 20 Daga APC: Ku Nemawa Kanku Mafita Tun Kafin Wuri Ya Kure Maku – Hon. Ɗanlami Kurfi

Kamar yadda rahotanni ke cewa akwai kusan Sanatoci 20 na jam'iyyar APC da ke kokarin ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai da suka ƙi...

MATSALAR TSARO: Yanda Al’umar garin Mada, dake ƙaramar Hukumar mulkin Gusau suke barin gidajen su…

Matsalar Tsaro: Yadda al'umar garin Mada dake karamar hukumar mulkin Gusau ta jihar Zamfara ke barin matsugunnansu a safiyar yau Asabar sakamakon ta'azarar hare-haren...
%d bloggers like this: