Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal ya yi karin haske game da makomar sa bayan wa’adin mulkin Gwamna Masari

Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal ya nisanta kan shi daga wasu fastoci dauke da hotunan shi da aka wayi gari an manna a wasu wurare cikin birnin Katsina ana cewa ya tsaya takarar kujerar majalisar dattawa ta Katsina ta tsakiya.

Muntari Lawal wanda babban aminin Gwamna Masari ne shekaru da dama da suka wuce ya ce bai taba tunanin tsayawa neman takara ta neman ko wane irin mukami ba.

Ya kara da cewa har yanzu yana a kan matsayin sa na yin biyayya ga Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari kuma ba zai taba neman wata kujera ba alhalin ana tsaka da kokarin fita kunyar yan jihar.

Muntari Lawal wanda kuma shine ya jagoranci kwamitin shirya zaben shugabannin jam’iyar APC a jihar Katsina ya kara da cewa masu neman kawo rikici a cikin jam’iyar APC a jahar ne ke yada irin wannan labarin wanda ya kira wani nau’i na cin mutunci da kuma wulakanci.

Daga karshe kuma ya yi kira ga mutanan jihar Katsina da cewa shi yana nan a kan bin Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari sau da kafa, kuma idan Gwamnatin ta gama wa’adin ta, to zai koma gona kamar yadda Gwamna Masari yayi alkawari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here