Advert
Home Sashen Hausa Ngozi Okonjo-Iweala: Tsohuwar ministar kudin Najeriya na dab da zama shugabar WTO

Ngozi Okonjo-Iweala: Tsohuwar ministar kudin Najeriya na dab da zama shugabar WTO

Ngozi Okonjo-Iweala: Tsohuwar ministar kudin Najeriya na dab da zama shugabar WTO

Ngozi Okonjo-Iweala

Jekadun kasashe a ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya WTO sun gabatar da sunan tsohuwar ministar kuɗin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar.

Idan dai har aka zaɓi Ngozi Okonjo-Iweala, za ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da ta taba riƙe mukamin a tarihin ƙungiyar.

Ngozi ta samu goyon bayan jakadun ƙasashe, Haka ma ta samu goyon bayan Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka.

Ngozi na fafata wa ne da Ministar Kasuwanci ta Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee a zagayen ƙarshe na takarar kujerar shugabancin Ƙungiyar.

Ƙasar Amurka na adawa da zaɓen Okonjo-Iweala, inda ta ke goyon bayan ƴan takara daga Koriya Ta Kudu Yoo Myung-hee.

GREENTIDE AGRO
Advertisement:GREENTIDE AGRO

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

MUN GANI A KASA A HUKUMAR KASROMA ~~~Cewar Alhaji Salisu Mamman CONTINENTAL

A ranar 18 ga watan Oktoba ne na shekarar 2021 wata Kungiya mai zaman kanta da ake kira "Mun Gani A Kasa" ta shirya...

Top 10 richest states in Nigeria;

Top 10 richest states in Nigeria; 1. Lagos - $33.68 billion Lagos tops the list of the top 10 richest states in Nigeria. It is also...

Tsohon Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II da Sheikh Maƙari, Babban limamin Abuja Sun garzaya Senegal wajen bikin Mauludin Annabi S.A.W

Sarki Muhammadu Sanusi Lamido da Sheikh Makari sun shilla kasar Senegal domin halartar Maulid Annabi Muhammadu SAW. Rahotanni Cikin Hoto na Cewa Mai martaba sarkin...
%d bloggers like this: