NDLEA (ta kama koken da ba’a taba cafkewa irinta ba a shekara 15)

DP

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama hodar koken da ta kai darajar naira biliyan 30 a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Daya daga cikin kayan da aka kama ya kai nauyin kilo 26.840, wanda shi ne abin da aka taba kamawa mafi girma a hannun mutum guda cikin shekara 15 a Najeriya.

Hukumar ta wallafa wannan kamu ne a shafinta na Twitter, tana cewa wata mace ce mai shekara 33 ke da kayan.

Da misalin karfe 1:20 na ranar 27 ga watan Janairu aka kama wannan ka ya a cikin fasinjojin jirgin Ethiopia, wadda ta taso daga Sao Paulo na Brazil na Brazil.

’’Wadda ake zargin, mai gyaran gashi ce a Brazil, ta amince cewa an bata aikin kawo wadannan miyagun kwayoyi akan naira 2,000,000.

Ko da yake dai taki ta bayyana sunayen wadanda suke aiki tare, amma ta ce an bata umarnin cewa ta mika kwayoyin ga wani. Da wadannan kayan sun tsallake, za su kai darajar naira biliyan 21. In ji wani jami’in hukumar.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here