Advert
Home Sashen Hausa Nayi mafi girman Nadama akan Hotona da na wallafa a shafina-Rahama Sadau

Nayi mafi girman Nadama akan Hotona da na wallafa a shafina-Rahama Sadau

RAHAMA SADAU TAYI DANA-SANI AKAN HOTUNAN DA TA SAKI A KAFAFEN SADA ZUMUNTA.

Kamar yanda ta Rubuta a Shafinta na Facebook; banji dadi ba yanda naga wasu, sunyi mummunar fahimta a gareni ta hanyar aiko min da saƙonni na ɓatanci akan hotuna da na wallafa marasa cutarwa a matsayi na ta mutum ƴar adam.

Wasu sun fusatani wasu kuma sun sani dariya, abinda yafi bani takaici da yasanya ni ɓacin rai gami da da nasani shine yanda wasu masu banbancin addini (waɗanda ba musulmi ba) sukayi maganganu masu nauyi na cin mutunci ga Annabi da Addini.

Na barranta da Irin waɗannan kalaman bana tare da duk masuyi nakumayi nadama da danasani akan abinda ya biyo baya.

Ina tare da duk wata ma’ana ta gaskiya tare da raba kaina da irin waɗan’nan kalaman na ɓatanci da cutarwa.

Ga duk wanda ya sanni ko yake bibiyata yasani cewa niba me maida Raddi ga wani zance na ɓatanci da akai mani, ko biyewa masu ɓatanci bace.

AMMA FA AKAN ANNABI NA NAN NE ZAN SHATA LAYI, “zan iya ɗaukar duk wani cin mutunci akan kaina Amma banyarda da ataɓa mutuncin Annabi na ba”.

Duk wani rashin girmamawa ga Addini na da Annabi na dangane da waɗan’nan Hotunan Inaci gaba da la’antar su da yin Allah wadai akan masu aikatawa.

Yakamata ne su masu yin wan’nan ɓatancin suzama masu magana akan haɗin kan Al’uma ba rabawa ba yakamata ne su koyi mutunta Imanin kowa, domin zaman lafiya.

Na kasance mai ƙauna da kishin Annabi na azuciyata (baɗina da zahirina) kuma ga duk mai bin shafi na na yanar gizo zai fahimci nadama ta, da dana sani na a fili, nayi kuskure Ina neman afuwa kuma zanci gaba da neman afuwa, kuma kusani cewa ni abinda nayi ba don naci mutunci wani ba sai don raha da barkonci, saboda ni ƴar Film ce.

Aƙarshe ina godiya ga waɗanda suka kirani ta waya da sauran kafafe domin nusar dani akan kuskure, wan’nan itace soyayyar gaskiya, ina tare daku.

Ga masu munanan kalamai da yimun cin mutunci, bana maku fatan abinda kuke fata akaina, tsawon rayuwa da Aminci inama kowa fatan Alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

BALA ABU MUSAWA NE ZABINMU ~~~Gamayyar Kungiyoyin Goyon Bayan APC na Shiyyar Daura

Daga Bishir Mamman @ katsina city news Kungiyar wadanda suke da wakilci a kananan hukumomin yankin sanatan Daura, karkashin shugabancin Sani Abdurrahman da mataimakiyarsa Hadiza Mamman. Suna...

POLICE ARREST SEVEN FOR KIDNAP, INFORMANTS.AND SUPPLY OF FUEL

Hassan Male @ Katsina city news The Katsina State Police Command had on the 18/9/2021 succeeded in arresting one Lawal Shu’aibu ‘m’ aged 32 years of...

ARREST OF SUPPLIERS OF FUEL TO BANDITS

On the 18/9/2021 based on credibleintelligence, the command succeeded in arresting (1) Lawal Shu'aibu 'm' aged 32 years of Maradi, Niger Republic. Conveying fuel...

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA ...A tabbatar Da An Yi Adalci *Jinjina Ga Gwamnan Katsina Da Alhaji Muntari Lawal @Katsina City News Ranar Asabar 2...
%d bloggers like this: