Nasiru El’rufa’i Butulu ne- Ayuba wabba.

Shugaban kungiyar kwadago na ƙasa yau a Kaduna wajen Zanga-zanga.

 

@Katsina City News

Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya Comrde Ayuba Wabba yace Idan kukaga baninan ko na ɓata to Nasiru El’rufa’i ne saboda yace yabada kudi a kamani, kuma na sanar da IG da hukumomin da suka dace,

Yanada kyau a binciki El’rufa’i baya rasa wani waje da suke ɓatar da mutane saboda mungani sun kama wasu sun ɓatar, yace idan ankamani a akaini Ministry of justice to dama adoka haka akeyi? Ya tambaya.

El’rufa’i Butulu ne saboda a 2012 yazo wajena a bayan ya dawo daga guduwa da yayi ya sameni a Bega jakshin da T-shirt kai ba hula yace intaimake shi, yasani babu wanda zai iya kwatar ‘yancinsa sai kungiyar kwadago, (NLC) yace ita kaɗai ce zata iya cetar mutanen Najeriya da kuma shi.

Don haka munshirya kuma nabada Notis zamu fito duk faɗin Najeriya muyi zanga-zanga mu shiga yajin aiki domin kwatowa talakawa ‘yancin su, saboda an ƙara kuɗin makaranta da da Asibitoci, dalibai basa iya karatu wasu ma ankoresu daga karatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here