Home Sashen Hausa NASARORIN SOJAN SAHEL SANITY DAGA SATUMBA ZUWA OKTOBA..

NASARORIN SOJAN SAHEL SANITY DAGA SATUMBA ZUWA OKTOBA..

NASARORIN SOJAN SAHEL SANITY DAGA SATUMBA ZUWA OKTOBA..

Daga Aminu ilyasu

A cigan yunkurin dakarun sojojin kasa na Najerimya domin kawar da miyagun ayyukan yan bindiga dadi, masu garkuwa da mutane, barayin dabbobi da yawan kashe – kashen da ya addabi al’ummar yankin Arewa maso Yamma na kasar nan, sojojin Operation SAHEL SANITY suna ci gaba da kara kaimi domin dakile wadannan miyagun ayyuka a fadin yankin baki daya a daidai wannan lokaci. Wannan kuwa ya kai ga dakile ayyukan miyagun kamar yadda yake a zahiri dangane da nasarorin da aka samu a wannan lokaci wanda ya jawo komowar ayyukan noma da hada-hadar jama’a ta yau da kullun.

Kawo yanzu, dunbin nasarorin da sojojin Operation SAHEL SANITY suka samu na nuni da jarunta, kishin kasa da jajircewar su inda abin takaici wasu daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya cikin gudanar da aikinsu. A cikin wannan lokaci, zaratan sojojin Operation SAHEL SANITY sun sami nasarar kaddamar da suntirin dare da rana, kwantan bauna gami da ragargaza maboyar yan bindiga dadi, inda wannan ya jawo hana miyagu cin karen su ba babbaka da walwala. Haka zalika, sojojin sun kaddamar da sunturi a gonaki da manyan hanyoyi a jihohin Sokoto, Katsina, Kaduna, Kebbi da Zamfara domin samarwa manona da matafiya cikakken tsaro. Mafi mahimmanci, wannan atasaye ya yi nasarar kubutar da dunbin wadanda ake garkuwa da su, hallaka gungun yan bindiga dadi tare da kame masu basu bayanai da kayan masarufi. Haka zalika an samu nasarar kwato shanun sata masu dinbin yawa gami da mayardasu ga masu su. Kazalika, sojojin sun kwato dunbin makamai da harsasai gami da miyagun makamai daga hannun yan bindiga dadin yayin fafatawa dasu. Bugu da kari, dakarun sojojin sun ragargaza maboyar yan bindiga dadi da kayan aikinsu a lokuna daban-daban cikin dazuzzukan yankin a cikin wannan lokaci.

Kawo yanzu, a dukkanin atasayen da aka gudanar daga 4 Satumba zuwa 25 Oktoba 2020, an hallaka yan bindiga dadi 38 yayinda kuma aka cafke masu taimaka musu da bayanai da kayan aiki guda 93. Haka zalika, sojojin sun kwato bindigogi kirar gida guda 30 gami da harsasai kirar 7.62 mm Special guda 941 tare da harsasan gajeriyar bindiga guda 5 yayin fafatawa da masu laifin a wurare daban-daban. Kazalika, sojojin sunyi nasarar kwato shanun sata 131, kananan dabbobi 154 gami da rakumi daya. A wani bangare, an sami nasarar ceto wadanda ake garkuwa da su har mutum 108. An cafke masu taimakawa yan bindiga dadi 90 gami da dillalan shanun sata 3. Haka kuma an ragargaza maboyar yan bindiga dadi 12 tare da dakile hare-haren yan bindiga kan al’ummar yankin har sau 47 gami da harin satar mutane sau 31.

Yanzu haka dai, zaratan sojojin Operation SAHEL SANITY na ci gaba da kaiwa da kawowa a daukacin yankin domin dakile duk wata barazana ga al’umma.

Domin haka, an yabi dakarun domin tsayiwarsu da dagewa wajen kare jamaa da dukiyoyinsu domin dorewar zaman lafiya da walwala. Haka kuma, an roki jamaar yankin da su ci gaba da baiwa sojojin hadin kai wajen basu bayanai da zasu taimaka a cimma karshen yanayin rashin tsaro a yankin baki daya kamar yadda kungiyar sojojin kasa ta Najeriya tayi alwashi.

Ga kungiyoyin yan darida na kusa da ma na nesa, muna masu yaba wa kwazo da sadaukarwarku. Muna masu fatan zamu ci gaba da cudanya da fahimtar juna domin daga martabar kasarmu.

Mun gode, Allah ya saka da alkhairi.

AMINU ILIYASU
Colonel
Nigerian Army Operations Media Coordinator
26 October 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: