NASARORIN DA SOJAN SAHEL SANITY SUKA SAMU A WATAN NAWUMBA.

Fassarar taron manema labarai

1. Jamaa barkanku da isowa wannan zaure namu a nan garin Faskari inda muka saba bayyana muku ayyukan wannan Runduna ta OPERATION SAHEL SANITY da ta dukufa wajen kawar da miyagun ayyukan Y’an Bindiga Dadi da sauran laifuffuka a yankin Arewa maso Yamma na kasar nan. Kamar yadda kuka sani, a tsakanin wannan lokacin, dakaru sun tsananta farmaki kan miyagu ta hanyar kakkabe su da fatattakar su daga maboya, gudanar da kwanton bauna kan miyagu tare da cafke masu basu bayanai da kuma wasu dabarun soja daban-daban domin kare al’ummar wannan yanki.

2. Babu shakka, wadannan atasaye da sojojin ke gabatarwa sun kai ga cimma dunbin nasarori kamar hallaka wasu daga cikin gagararrun Y’an Bindiga Dadi, kwato miyagun makamai, ragargaza maboyar miyagu, kame masu baiwa miyagu tallafi da kuma mafi mahimmanci, kubutar da mutane da ake garkuwa da su.

3. Wasu daga cikin nasarorin da dakarun suka samu a wannan lokacin sune:
A ranar 15 ga watan Nuwamba 2020, dakarun rundunar OPERATION SAHEL SANITY sunyi arangama da Y’an Bindiga Dadi yayin da suke gudanar da sunturin dare a kauyen Y’ar Tasha dake a karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara. Wannan arangama da zaratan sojojin ta kai ga hallaka 3 daga cikin miyagun gami da kwato bindigogi 3 kirar AK 47 da alburusai nauin 7.62mm Special yayin da wasu daga masu laifin suka sha da kyar. Haka zalika, a ranar 16 ga watan Nuwamba 2020, zaratan sojojin OPERATION SAHEL SANITY sun sami bayanin ayyukan danyen aikin masu garkuwa da mutane a garin Arawa dake karamar hukumar Tangaza a Jihar Sakwkwato inda suka zabura suka kuma dakile mugun nufinmiyagun. A yayin wannan gumurzu, dakarun sunyi nasarar hallaka daya daga cikin masu garkuwar da mutane gami da kwato bindiga kirar AK 47 guda daya da babur guda daya yayinda sauran masu laifin suka tsallake rijiya da baya.

4. A wani bangaren, a ranar 21 ga watan Nuwamba 2020, zaratan dakarun OPERATION SAHEL SANITY sun kaddamar da samame kan maboyar Y’an Bindiga Dadi da aka gano a kauyukan Mararrabar Kawaye da Gobirawa a cikin karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina inda dakarun suka ragargaza maboyun nasu bayan yin nasarar hallaka 6 daga cikin Y’an Bindiga Dadin. Haka kuma dakarun sun kwato bindigu 4 kirar AK 47 gami da bindigu 3 kirar gida da babura guda 2. Sojojin na ci gaba da dakushe amon miyagun a yankin baki daya.

5. Haka zalika, a ranar 21 ga watan Nuwamba 2020 sojojin OPERATION SAHEL SANITY sun yi fata-fata da wata maboyar Y’an Bindiga Dadi a kauyen Galadi dake karamar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara bayan samun bayanan sirri. A yayin wannan fafatawa dai, Y’an Bindiga Dadi 2 sun tafi barzahu. Haka kuma, yayin da dakarun sojojin suka tsananta bincike a maboyar, sun zakulo bindigogi 2 kirar AK 47. Kazalika, a ranar 22 ga watan Nuwamba 2020, sojoji sun yi arangama da wasu Y’an Bindiga Dadi lokacin da suke sunturi a gonaki domin kare lafiyar manona a yankin Gidan Ruwa na karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara. Miyagun sun bude wuta kan zaratan sojojin domin neman tserewa amma duk da haka jaruman sojojin suka bisu da aman wuta inda suka hallaka daya daga cikin Y’an taaddan yayin da saura suka tsere. Sojojin sun yi nasafar kwato bindiga guda daya kirar AK 47 tare da alburusai nau’in 7.63mm Special guda 29 a yayin wannan arangama.

6. A wani bangare, a ranar 12 ga watan Nuwamba 2020, sojojin OPERATION SAHEL dake kula da shiyyar Faskari sun damke mutane 2 masu suna Lawal Madawaki da Hassan Ali a kauyen Gobirawa dake cikin karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina wadands bayanai suka nuna cewa suna baiwa Y’an Bindiga Dadi bayanan sirri. Hakazalika, a ranar 13 ga watan Nuwamba 2020, sojojin sun yi amfani da bayanan sirri inda suka cafke wasu masu tallafawa Y’an Bindiga Dadi su uku masu suna Abdulmumini Maidoki, Lawal Abdullahi da Sanusi Abdullahi a kauyen Majafa dake karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina. Haka kuma an damke wasu mutum 2 masu suna Lawal Danladi da Rane Bello yayin wani samame da sojojin suka Kai a wata maboyar Y’an Bindiga Dadi a kauyen Maikano na karamar hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

7. A dai wannan rana, dakarun sun sami nasara cafke wani wanda yayi fice gurin baiwa Y’an Bindiga Dadi bayanan sirri mai suna Bello Ardo a kauyen Y’argoje dake karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina. Haka zalika, a ranar 22 ga watan Nuwamba 2020, dakarun sojojin sun kaddamar da wani samame kan wata mahakar ma’adan sata dake Kadauri a cikin karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara inda suka damke barayin ma’adanai 11. Kazalika, a ranar 24 ga watan Nuwamba 2020, dakarun OPERATION SAHEL SANITY sun yi amfani da bayanan sirri inda suka binciko sansanin barayin shanu a kauyen Dankori dake karamar hukumar Mani ta Jihar Katsina inda suka kame mutum 3 tare da kwato shanun sata 300.

8. A wata sabuwar, a ranar 28 ga watan Nuwamba 2020, dakarun OPERATION SAHEL SANITY dake sunturi sun kame Y’an Fashi 4 sanye da kaya masu ganye-ganye irin na sojoji a kauyen Macrine dake cikin karamar hukumar Yelwa ta Jihar Kebbi. Dukkan masu laifin dai an mika su ga hukumomin da zasu gurfanar da su gaban sharia.

9. A takaice, a jimlar atasayen da sojojin OPERATION SAHEL SANITY suka gabatar daga 12 – 29 ga watan Nuwamba 2020, sun sami nasarar kakkabe Y’an Bindiga Dadi 12 tare da kwato bindigogi 11 kirar AK 47 da bindigogi kirar gida 3. Haka zalika, an cafke masu taimakawa Y’an Bindiga 8 gami da marayin ma’adanai 11 da da barayin shanu 3. An kuma sami nasarar kwato shanun sata 300.

10. Hukumar sojan Najeriya na matukar godiya ga mazauna wannan yankin domin goyon bayan da suke baiwa wannan runduna wajen samun wadannan nasarori. Hukumar na ci gaba da neman goyon bayan su domin karasa kakkabe miyagun da suka saura a wannan yankin.

11. Ga abokanan mu yan jarida, muna masu jinjina muku da godiya ta musamman domin kwazon ku gurin aiwatar da ayyukan domin amfanin al’umma baki daya. Mun gode, Allah ya kai ku gidajen ku lafiya.

AMINU ILIYASU
Colonel
Nigerian Army Operations Media Coordinator.
4 December 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here