Nasarori da sojoji suke samu na yakar yan ta’addan Arewa maso yammacin Najeriya.

1. Umurnin share duk wasu ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane shiyyar Arewa maso Yammacin kasar nan, na ci gaba da samar da kyakkyawan sakamako ayayin da rundunar Operation SAHEL SANITY a cikin samamen baya-bayan nan a maboyar ‘yan taddan suka samu karin nasarori a kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a yankin.

2. A ranar 18 ga Satumbar 2020, sojoji da aka tura a Dangulbi yayin da suke gudanar da aiki na yau da kullun a wani yanki da aka gano yan ‘yan bindiga, sun kama mutane 2 da ake zargi Umaru Lawali da Ahmed Bello. Abubuwan da aka kwato daga wurin su sun haɗa da bakar safar rufe fuska 2  (waɗanda ake zargi da amfani da su yayin aikata laifi), da tabar wi-wi da babur ɗaya.

Har wayau, sojoji sun kama wani mai suna Abdullahi Lawal da Bala Saidu a Sabon Layi da Dandume, ana zargin suna sayar ma da barayin shanun da suka sata, Hakanan sojojin da aka girke a Kwatarkwashi da ke jihar Zamfara suna aiki da wani ingantaccen bayani sun kama wani Yunusa Muhammad a Gidan Yawa da ke karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara. Wanda ake zargin, ya amsa laifinsa cewa shi kwararre ne wajen shirya sace mutane tare da karbar kudin fansa a madadin ‘yan fashin.

3. Bugu da kari, a ranar 19 ga Satumbar 2020, sojojin da aka tura a Dandume suna aiki da sahihan bayanai sun dakile wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kaia karamar hukumar ta Dandume da ke jihar Katsina. Sojojin da suka samu bayanai kan lokaci na yadda wadanda ake zargin ke tafiya tare da babura sun hanzarta zuwa yankin tare da yin musayar wuta da ‘yan ta’addan.

Karfin sojojin ya tilasta guduwa ga ‘yan bindigar da munanan raunika ajikin su a yayin da akaga alamun jini a kan hanyar su ta tserewa.

4. Hakanan, a ranar 19 ga Satumbar 2020, bayan ingantattun bayanai, sojojin da aka tura a Batsari sun kama wani da ake zargi da fashi da makami mai suna Abdullahi Musa a kauyen Giginyu. An gano cewa wanda ake zargin yana tare da ‘yan bindigar da ke addabar yankin.

Haka kuma, ankama  Amadu Saleh da Shaibu Ibrahim a kauyukan Madachi da Maigora. An tabbatar da wadanda ake zargin suna da hannu a fataucin haramtattu kayayyaki suna kaima ‘yan bindigar. Bugu da kari, bayan wani ingantaccen bayani game da motsin wasu mutane da ba a san su ba wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne da babura 6 a dajin Dan Aji da ke kusa da Yar Mallamai a karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina, nan da nan sojoji suka hada kai suka yi kwanton bauna a yankin kuma suka kame 6 da ake zargi daga cikin su.

5. Hakazalika, a ranar 19 ga Satumbar 2020, sojoji sun amsa kiran gaggawa game da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne suka afka wa kauyen Dayau da ke karamar hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara. Da ganin isowar sojoji, yan fashin suka gudu suka shiga daji, amma duk da haka sojojin da suka jajirce suka bi su har zuwa cikin dajin, inda suka fatattaki daya daga cikin yan fashin yayin da aka kwato babur daya daga hannun masu laifin. A wannan rana, sojojin da aka girke a Yar Tsamiya Jino yayin da suke sintiri sun ceto wata yarinya da aka sace da ake kira Jamila Sani a gefen iyakar dajin Yar Tsamiya Jino. Binciken farko ya nuna cewa an sace ta tare da wasu a kauyen Makasu da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina a ranar 7 ga Satumbar 2020. Ana ci gaba da kokarin ceto sauran wadanda abin ya shafa.

Ankamashi a karamar hukumar tsafe ana zargin yana baiwa ‘yan bindiga bayanai. Sunan sa Yunusa muhammad

6. Har ila yau, a ranar 20 ga Satumbar 2020, sojoji sun kama mutane 2 da ake zargi ‘yan bindiga ne wadanda suka hada da Dayyabu Abubakar da Yahaya Murtala a kan hanyar Machika zuwa Mararaba. Haka kuma, a ranar 22 ga Satumbar 2020, bayan wani bayani, sojoji a Faskari Jihar Katsina sun kame wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne 2 su ne Haruna Hassan da Kabiru Abdullahi a Kasuwar Yankara da Anguwan Boka. An gano wadanda ake zargin ‘yan kungiyar ta’adda ne da ke addabar mazauna yankin, kayayyakin da aka samu a wurinsu sun hada da wayoyin hannu 2, wuka daya da abar wiwi. A wannan ranar, sojojin na sashi na 3 sun cafke wani mai suna Mallam Gambo, wanda ake zargi da aika ma barayin bayanai a Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

7. Bugu da kari, a ranar 23 ga Satumbar 2020, sojoji a kan sintiri sun rusa sansanonin ‘yan fashi da yawa kuma sun kwato bindigogin Dane 2, da takobi a cikin gida da kuma Adduna 3. Hakanan, sojojin da ke aikin leken asiri sun kai samame wasu sansanonin ‘yan bindiga a yankin Gadawa. ‘Yan bindiga sun tsere daga yankin kafin sojojin su iso, duk da cewa, sojojin sun kwato babura 2, wayar hannu daya da kuma kudi Naira dubu Goma (N10,000.00) bayan sun gudanar da cikakken bincike a yankin. Hakanan, sojojin da aka tura a garin Daudawa sun kama wani da ake zargi da hada baki da ‘yan bindiga mai suna Abubakar Isah a kauyen Daudawa da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

8. Bugu da kari, a ranar 24 ga Satumbar 2020, sojoji da aka tura kauyen Dan Ali bisa sahihan bayanan sirri sun kama wasu mutane 9 da ake zargi ‘yan bindiga ne a yankin Sabon Garin Dan Ali da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina. Hakanan, sojojin da aka tura a garin na Daudawa, yayin da wasu mazauna yankin suka bayar da sanarwar sun kama wani mutum mai suna Surajo Bala, wanda ake zargi da kai rahoton ‘yan bindiga. Wanda ake zargi ya amsa cewa yana da hannu a shirya garkuwa da ‘yan bindigar. Hakanan, sojojin da aka tura a Safana, sun amsa kiran wani agajin gaggawa sun dakile wani harin yan bindiga kuma sun kwato shanu da yawa a kauyen Danyegeya da ke karamar hukumar Safana. Sojojin sun hanzarta kutsawa cikin kauyen suka bi ‘yan maharan tare da tilasta musu barin kayayyakinsu yayin da suke tserewa daga karkashin duhuwa tare da raunin harbin bindiga a jikin su. Shanun da aka kwato an mika su ga masu su, yayin da sojoji ke ci gaba da mamaye yankin tare da sintiri a lungu da sakon yankunan.

9. A karshen, an yaba wa zaratan sojojin na Operation SAHEL SANITY saboda nasarorin da suka samu da kuma jajircewa kan aiki. An kuma yi kira garesu da su kara kaimi har sai an kawar da duk wasu yan tadda da bata gari a Arewa maso Yamma Yayinda kuma aka sake tabbatar wa mutanen Arewa maso Yamma da sojojin sadaukar da kai don kare rayuka da dukiyoyin da ke yankin, an kuma karfafa musu gwiwa su ci gaba da ba sojojin hadin kai da bayanan da suka dace a kan kari,wanda zai taimaka musu don kawar da aiyukan ta’addanci a yankin.

10. Akwai hotuna na yanda barayin suka zo hannu, kuma muna godiya da hadin kan da jama’a ke badawa ta hanyar bayanai daga yankunan su.

BENARD ONYEUKO

Birgediya Janaral

Mukaddashin Darakta

Ayyukan Defence na Media

 

27 Satumba 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here