Advert
Home Sashen Hausa NASARA GA MUJJALAR KATSINA CITY NEWS DA JARIDAR DAILY TRUST

NASARA GA MUJJALAR KATSINA CITY NEWS DA JARIDAR DAILY TRUST

A ranar 16 ga Maris, 2019 ne, Wakilin jaridun DAILY TRUST na Katsina na lokacin, Umar Habibu ya rubuta wani a labari mai taken: ‘Ziyara a garin Dumurkul’. Asalin inda aka haifi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A fitowar mujjalar KATSINA CITY NEWS, ta wata MarIis, 2021 ta sake buga wannan mukala kamar yadda DAILY TRUST ta kawo ta a 2019 babu wani canji ko gyara, ta kuma ba shi muhimmacin saka shi gaban bangon na fitowar ta.

Tsarin mujjalar tana kai wa duk wani muhimmin mutum daga Katsina a ko’ina yake, Abuja, Legas da sauransu.

A fitowar ta ta Maris, 2021, ta aika wa Kakakin Majalisar dokokin Katsina, inda kowane Dan Majalisa ya samu kwafi da Majalisar Tarayya da ‘yan Katsina masu rike da muka da mazauna wajen Katsina.

Wannan fitowar ta yi yawo sosai. Don haka labarin asalin inda aka haifi Shugaban Kasa kowa ya san shi.

Ganin labarin ya sanya wasu suka yi fatan wannan gari na Dumurkul a mayar da shi Gudumar Hakimi don girmamawa ga Shugaban Kasa.

A ranar 8/7/2021, Gwamnan Katsina ya aika da bukatar gaggawa ga Majalisar Dokokin Jihar na mayar da yankin Dumurkul da ke karkashin Koza a Karamar Hukumar Mai Aadua ta zama Gunduma mai mukamin Hakim.

A ranar 26/7/2021 Majalisar Dokokin har Katsina ta mayar da Gundumar Dumurkul mai darajar Hakimi a zaman ta na gaggawa.

Mu a mujallun KATSINA CITY NEWS, wannan ya kara mana karfin gwiwa a kan rahotanni bin diddigi da binciken kwakwaf.

Za mu ci gaba da dauko rahotonni masu amfani da kawo wa Jiha da Kasarmu ci gaba in Allah ya yarda.

Muhammad Danjuma,
Babban Editan
Jaridun Katsina City News da ke yanar gizo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: