Nasamu Damar da Zan’iya guduwa daga hannun Masu garkuwa da Mutane, amma saboda tausayin yarinyar waje na yasa naci gaba da binsu….Inji Ahamad Abdulkadir Bakori

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 3/12/2021

Ahamd Abdulkadir Bakori tare da Yarsa Laila bayan sun kubuta daga masu garkuwa da Mutane

A watannin da suka gabata ne, Allah ya kuɓutar da tsohon Darkata a ma’aikatar kula da gidajen Rediyo da Talabijin ta ƙasa NBC wato Alhaji Alhaji Ahmed Abdulƙadir daga Hannun masu garkuwa da Mutane, inda ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da shi, da diyarsa na tsawon kwanika kafin Allah ya tseratar da shi…

Jaridar Katsina City News ta samu zantawa dashi, kai tsaye ta Hoto mai Motsi (Video) inda ya sheda mana irin yanda suka zo gidansa dake garin Bakori, har suka tafi dashi da diyarsa Laila ‘uar kimanin shekaru sha shida, dakuma Irin wahalar da suka sha, har zuwa lokacin da Allah ya kubutar dasu.

Ga masu bibiyar Shafin mu na YOUTUBE zaku iya samun firar cikakkiya, mai cike da darasi, gami da shawara ga mahukunta, a matsayinsa na jami’in yada labarai, da kuma irin abinda ya gani kuru-kuru da idonsa.. ku biyomu a shafin namu domin ji daga bakinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here