Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da sauya wajen aiki ga Bashir Garba Lado, daga Kwamishinan Hukumar kula da ‘Yan Gudun Hijira da jin ƙai ta ƙasa, zuwa Darakta Janar na Hukumar Hana safarar Bil’Adama, wato NAPTIP.

Sabon Shugaban Hukumar NAPTIP Sen. Bashir Lado

A cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Garba Shehu ya fitar, ta ce Buhari ya kuma sauyawa Darakta Janar ta Hukumar ta NAPTIP, Imaan Sulaiman, wajen aiki, zuwa Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, a matsayin Kwamishina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here