Najeriya na shirin rancen dala miliyan 750 don tallafawa talakawa a jihohi

Najeriya na kan hanyar samun rancen dala miliyan 750 daga Bankin Duniya domin bai wa jihohin ƙasar damar tallafawa talakawa da nufin rage raɗaɗin tasirin annobar korona ga tattalin arziki.
Ma’aikatar kuɗin kasar ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.
Babban Bankin Najeriya a watan Yuni ya ce annobar korona ta jefa ƴan Najeriya miliyan biyar cikin talauci baya ga taɓarɓarewar tattalin arziki mafi muni da ƙasar ta shiga tun 1980.
An bayyana cewa kuma Najeriya na kan tattaunawa da Bankin Duniya kan rancen dala biliyan 1.5 don taimakawa kasafin kuɗinta.