Najeriya za ta karɓi riga-kafin korona a watan Janairu

Najeriya na sa ran samun riga-kafin cutar korona nan da ƙarshen watan Janairu yayin da take ƙoƙarin kare kashi 40 cikin 100 na al’ummarta daga cutar a wannan shekarar da kuma kashi 30 a shekara mai zuwa.
Zubin farko zai ƙunshi allurar guda 100,000 ta Pfizer-BioNTech, wadda wani shirin Majalisar Ɗinkin Duniya zai samar mai suna Covax.
Da farko ƙasar za ta fara yi wa ma’aikatan lafiya riga-kafin da masu kai agajin gaggawa da shugabanni da mutanen da ke da wasu cutuka da kuma tsofaffi, a cewar shugaban hukumar lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib.
Ƙasar na fatan samun guda miliyan 42 da za ta ishi ɗaya bisa biyar na jama’arta, a cewarsa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ƙaddamar da shirin Covax ne domin taimaka wa ƙasashe marasa ƙarfi saboda fargabar ƙasashe masu arziki za su wawashe ta.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya faɗa a makon da ya gabata cewa ƙasarsa za ta karɓi riga-kafin ta shirin Covax nan da tsakiyar 2021 bayan ta fara biyan miliyan 283 na kuɗin ƙasar (dala miliyan 19).
Mutanen da suka harbu da cutar korona a Najeriya sun kai 92,705 sannan an sallami mutum 76,396 daga asibiti bayan an tabbatar sun warke, yayin da 1,319 suka mutu tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.