Najeriya: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Sansanin Soji Hari A Zamfara

Wata Motar yaƙin da Mahara suka ƙona a Zamfara

Wani rahoto ya Najeriya: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Sansanin Soji Hari A Zamfara ‘yan bindiga sun kai hari kan wani sansanin soji a cikin jihar Zamfara a arewacin tarayyar Najeriya.

Jaridar Premium Times ta sheda cewa, wasu majiyoyo sun tabbatar mata da kai harin, inda mahara suka dira kan sansanin sojojin da ke Mutumji, Karamar hukumar Dansadau ranar Asabar da ta gabata.

A cewar rahoto wannan harin ya yi sanadiyyar rayukan sojojin sama 9, ‘yan sanda biyu da sojan kasa 1.

Bayan kashe jami’an tsaro da ‘yan bindiga suka yi, sun kwashe makaman sojojin da suka kashe sannan suka banka wa sansanin wuta gaba daya.

Ko a cikin makon jiya ma, ‘yan bindiga sun harbor jirgin yaki da ke ruwan wuta a kansu, duk kuwa da cewa bayanin da rundunar sojin Najeriya ta bayar, ya tabbatar da cewa direban jirgi ya tsira da ransa.

Sojoji da jami’an tsaron Najeriya dai suna kaddamar da gagarumin farmaki a cikin dazukan Zamfara, inda suke farautar ‘yan ta’adda masu kisan jama’a da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa, ko kuma satar shanun mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here