NAJERIYA TAFI JAMUS?

Najeriya ta fi Jamus?

Wani dan Najeriya da ke koyarwa a jami’ar Kolon da ke Jamus Muhsin Ibrahim ya ce ya fi gamsuwa da tsarin bankin Najeriya a kan na Jamus. Ibrahim ya ce a Jamus idan mutum ya tura kudi daga wannan banki zuwa wancan sai sun yi kusan sa’o’i 24 kafin su isa sabanin Najeriya da nan take kudin ke shiga. Malamin jami’ar ya ce a Najeriya tun lokacin da Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya fito da sauye-sauye a harkar bankunan kasar, tsarin bankunan Najeriya ya zama mai sauki fiye da wasu manyan kasashen duniya. Shin kuna da ja a kan wannan? Wane irin abu ne kuke ganin dan Najeriya da sauran kasashen Afirka ya kamata ya rinka tutiya da shi cewa shi ma kasarsa ta sha gaban wasu manyan kasashen duniya?

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: