Najeriya ta yi tayin shiga tsakani a rikicin Chadi

Shugaba Buhari na Najeriya

Najeriya ta bayyana damuwa kan halin da ƙasar Chadi ke ciki inda ta yi kiran kai zuciya nesa tare da hawa teburin tattaunawa.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar mai ɗauke da sa hannun ministan harakokin wajen Najeriya Geoffery Onyeama, Najeriya ta yi tayin shiga tsakani domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Najeriya ta ce za ta yi jagorancin tattaunawar ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ƙasashen yammacin Afrika Ecowas da kuma Tarayyar Afrika AU.

“Ya kamata gaggauta dawo wa kan mulkin dimokuraɗiyya ya zama babbar manufar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Chadi da ƙasashen gabashin Afrika da na ƙasashen yammacin Afrika da kuma yankin Sahel,” a cewar sanarwar.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here