Najeriya ta sanar da ranakun hutun Kirisimeti da sabuwar shekara

..

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranakun hutun Kirisimeti da sabuwar shekara.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar, ranakun Juma’a 25 ga watan Disamba da Litinin 28 ga watan Disamban 2020 da kuma 1 ga watan Janairun 2021 za su kasance ranakun hutun Kirisimeti da ranar rabon kyaututtuka (Boxing Day) da kuma sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Rauf Aregbesola ya ja hankalin Kiristoci da su yi koyi da halaye na gari na Yesu Almasihu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here