BBC Hausa

Najeriya ta dakatar da bayar da sabon fasfo har sai an gama bai wa waɗanda suka nema nan da mako biyu masu zuwa.

Yayin da yake yi wa ‘yan jarida jawabi a Abuja ranar Talata, Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Immigration, Mohammed Babandede ya ce za a fara karɓar buƙatar yin sabon fasfon daga ranar 1 ga watan Yuni.

Babandede ya ce sun ɗauki matakin ne biyo bayan umarnin da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya bayar.

“An dakatar da ayyukan bayar da sabon fasfo a ƙasa baki ɗaya har zuwa 1 ga watan Yunin 2021, lokacin da za a fara amfani da sabon tsarin fasfo,” a cewarsa.

“An yanke shawarar dakatarwar ce saboda a gama bai wa dukkan waɗanda suka nemi a ba su fasfo ɗin tun daga 17 ga watan Mayu.”

Ya ce an rufe baki ɗayan hanyoyin biyan kuɗi har zuwa 1 ga Yuni, sannan za a tura tawaga ta musamman domin kammala aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here