Najeriya ta buƙaci a saki shugabannin Mali bayan juyin mulki

Buhari

Gwamnatin Najeriya ta yi tir da kama shugabannin Mali da sojojin ƙasar suka yi, tana mai bayyana shi da “abin da ba za a amince da shi ba”.

Cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Waje, gwamnatin Najeriya ta ce kama Shugaba Bah Ndaw da Firaminista Moctar Ouane zai kawo tsaiko wajen mayar da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya.

“Gwannatin Najeriya na kira da a saki shugaban ƙasa da firaminista nan take ba tare da wani sharaɗi ba,” a cewar sanarwar.

“Waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin su sani cewa ƙasashe ƙawayen Mali na Allah-wadai da tilasta wa shugabannin ko kuma matsa musu su sauka daga mulki.”

A jiya Litinin ne sojoji suka tsare shugaban Mali na riƙon ƙwarya da firaministansa jim kaɗan bayan sanar da yunƙurin kwaskwarima a majalisar ministocin ƙasar, wanda zai sa a sauya manyan sojoji biyu da suka yi juyin mulki a bara.

Za a kori tsohon ministan tsaro Kanar Sadio Camara da kuma ministan harkokin soja Kanar Modibo Koné daga majalisar.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here