Advert
Home Sashen Hausa Najeriya: Sarkin noman Zamfara ya ce za a yi shekara 10 noma...

Najeriya: Sarkin noman Zamfara ya ce za a yi shekara 10 noma bai farfaɗo ba a Jihar

Najeriya: Sarkin noman Zamfara ya ce za a yi shekara 10 noma bai farfaɗo ba a Jihar

Gona

Harkar noma ta shiga wani mawuyacin hali sakamakon hare-haren yan bindiga baya ga matsalar ambaliya da annobar korona da aka fuskanta.

A cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC na ranar Juma’a, Sarkin Noman Zamfara Alhaji Hassan Kwazo ya ce noman gaske da aka sani a Zamfara ya gagara saboda hare-haren ƴan bindiga.

Ya ce an ƙone wa manoman gidaje da gonaki, abin da ya sa suka watse, sai dai noman da ake na bakin hanya wanda bai wuce a noma buhu uku na hatsi ba ko kuma biyar.

“Ba a yi noman da aka saba ba kusan shekara biyar zuwa shida, noma ya ja baya a Zamfara, masu kuɗi waɗanda ke noma buhu 500 zuwa 1,000 gonakin sun gagare su zuwa,” in ji Sarkin Noma.

“Kuma kafin noman ya dawo kila za a kai shekara 10 saboda duk manoman da suke noman na gaske sun watse.”

Ya ƙara da cewa idan mutum ya tafi gona za a kama shi a yi garkuwa da shi, wannan ya sa manoman suka watse saboda har kananan manoma ake kamawa ana kashewa.

“Waɗanda ma suka samu suka ɗan yi noman, ɗan abin da suka samu na amfanin gona a hannun ɓarayin yake ƙarewa.”

A cewarsa kafin a yi noman ma sai an biya kuma babu garanti, idan an yi girbi sai an biya ɓarayin kafin su amince a girbe amfanin gonar.

“Wadanda suka ɗan yi noman a bakin hanya ne suke karo-karo da ƴan uwa waɗanda suka samu sa’a suka girbe amfanin gona suke haɗa kuɗi su sayar su je a biya kuɗin fansa a karɓo ƴan uwa da aka kama.

Barazanar ƙarancin abinci

Noma

Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ake hasashen za su haddasa ƙarancin abinci a arewacin Najeriya saboda yadda yan fashin daji da masu garkuwa ke addabar manoma suna hana su nome gonakinsu

Wannan na zuwa ne baya ga ƙalubalen da aka fuskanta na ambaliyar ruwa da kuma annobar korona.

Ana ganin ƙalunbalen tsaro da manoma ke fuskanta zai yi tasiri ga samar da abinci a Najeriya.

A cikin shirin Ra’ayi Riga, babban jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar manoma ta ƙasa, Alhaji Muhammad Magaji ya ce tabbas yankin arewa maso yamma na cikin matsala.

“A yankunan Katsina kamar Ɗanmusa da Safana da Bakori da Dutsinma, suna noma abinci kusan kashi 30 zuwa 35 na abin da ake samu a arewa maso yamma gaba ɗaya,” a cewarsa.

“Amma a yanzu noman ya gagara, manoma sun kasa zuwa gona. Da yawansu ba su yi girbi ba idan ma har sun yi noman.”

Ya ce hakan ya shafi yankunan Kaduna na Igabi da Birnin Gwari da Giwa da Kauro.

Wannan matsala suka ce za ta haifar da tsadar kayayyakin abinci a yankin arewacin Najeriya saboda rashin abincin.

Sarkin Noman Zamfara Alhaji Hassan Ƙwazo ya bai wa gwamnati shawara cewa ya kamata ta ɓullo da tsarin tallafa wa matasa na karkara, “waɗanda ke yin noma amma ake korewa daga gonakinsu kuma ake kashewa”.

Ya ce manomi ba bashi buƙata ba, idan aka ba shi tallafi da tsaro sun ishe shi.

line

Al’umma a Zamfara sun daɗe suna fuskantar hara-haren tare da ƙone garuruwansu daga ƴan fashi masu ɗauke da manyan bindigogi.

Hukumomi da jami’an tsaron sun sha iƙirarin cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya, amma har yanzu ana kai hare-hare da garkuwa da mutane duk da ikirarin gwamnatin Zamfara na yin sulhu da ƴan fashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: