NAJERIYA A YAU: ‘Illolin Kaurace Wa Zabe Sun Fi Na Kada Kuri’a Yawa’

Bayan ya dade yana jan hankalin hukumomi game da bukatar daukar mataki a kan rashin tsaron da ya gallabi ’yan Najeriya, wani limami ya yi kashedin cewa mutane ba za su fito zabe ba a 2023 idan ba a amsa wasu tambayoyi ba.
Da jin haka, kwamitin masallacin da Sheikh Nuru Khalid yake jan sallar Juma’a ya ce mallam ya wuce gona da iri, yana tunzura mutane kada su fito zabe.

Shirin Najeriya a Yau zai duba ya gani, ko kin fita zabe ne zai magance wannan matsala ko akwai wata mafitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here