Naira Marley ya fasa zanga-zangar neman rushe rundunar SARS
Mawaki Naira Marley ya fasa shiga zanga-zangar da ya ce ya shirya ta lumana kan cin zarafi da ‘yansanda ke aikatawa a kasar.
Mawakin a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ya soke gudanar da zanga-zangar saboda wasu sauye-sauye da aka samu.
Sannan ya ce sun ba da wa’adin mako guda domin ganin ko sauyin zai tabbata.
Ita ma rundunar ‘yansanda a wani sakon da ta wallafa a Twitter ta ce kakakinta, DCP Frank Mba zai tattauna da Naira Marley domin amsa tambayoyi da tattaunawa kan koken ‘yan kasa kai tsaye a shafin Instagram da misalin 11 na safiyar wannan Talatar.