NAF ta tabbatar da hatsarin Jirgi a Kaduna

Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya

Marigayi Gen. Ibrahim Attahiru Shugaban Sojojin Najeriya yana daya daga cikin wadanda suka mutu a Hatsarin

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta tabbatar da hatsarin jirgin ta, kusa da Filin jirgi na Kasa da Kasa dake Kaduna a yau Juma’a.

Rundunar ta tabbatar da hakan, a cikin wata sanarwa da Daraktan kula da Harkokin Jama’a ya fitar Edward Gabkwet.

A cikin sakon da ya fitar a shafinsa na twita yace” Hatsarin Jirgi daya rutsa da Manyan Hafsoshin tsaro ya faru ne kusa da Filin jirgi na kasa da kasa dake Kaduna. Har yanzu ba’a tabbatar da dalilin hatsarin jirgin. Amma zamu kawo cikakken bayani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here