NA KWASHE TSAWON SHEKARU 5 INA SIYAR DA MUSHEN KAJI A JIHAR BORNO-Inji wani Matashi

An yi nasarar kama wani magidanci wanda ake zargi da siyarwa da Al’ummar Jihar Borno, Mushen Kaji tsawon lokaci.

Jami’an hukumar Civil Defence ne suka yi nasarar cika hannu da shi.

Da yake amsa tambayoyi magidancin ya tabbatar da cewar a kalla ya siyar da Mushen Kaji guda dubu 6, a Jihar Borno da kewaye.

Magidancin dan kimanin shekaru 33, mai suna Hassan Ebere, ya ƙara da cewar ya kwashe a kalla shekaru 5 yana siyar da mushen.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar, har yanzu mutumin yana hannun Jami’an tsaro sai dai ya ce yana siyar da mushen ne don daukar nauyin kan shi tun bayan daya rasa mahaifin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here