Na haramta saka kiɗan fiyano a wajen taron Hausa, matuƙar ni ne uban ƙungiya – Farfesa Abdallah

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’a NOUN kuma mai ɗauke da matsayin Farfesa biyu a kan sa wato Farfesan Sadarwa da kuma Farfesan Kimiyyar Ilimi wato Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce daga yanzu indai an zo taron Hausa, kuma in dai an ce shi ne uban ƙungiya to ya haramta a saka kiɗan fiyano, amma ya ce idan ba za a yi haka ba sai a nemo wani uban amma ba shi ba, ya  ce hakan shi ne abinda zai burge shi.

Farfesa Abdallah ya yi wannan jawabi ne a taron ranar Hausa ta duniya da Jami’ar Bayero  ta shirya da ya gudana a Convcational Arena da sabuwar jami’ar da ke Kano, a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata, wanda shi ne karo na 6.

Farfesan ya ce “Na so a ce kamar yadda aka nuna gwanintar Bahaushe a abinci da maganin gargajiya, to ya kamata a nuna gwanintar Bahaushe a nishaɗi, to ga shi yau ban gani ba, na ga waqar Hausa mai daxi, amma ban ji kiɗan Hausa ba.

Farfesa Abdullah ya ci gaba da cewa “Muna da makaɗan gargajiyan da aka wofantar da su aka banzatar da su, kamar Nasiru Garba Super, yadda babansa ya ke kiɗan Garaya haka shi ma ya ke yi, akwai mata ma da suke kiɗan kukuma suke kiɗan garaya, inda za mu ɗauko mace mai shantu ta zo ta zauna ta yi mana waqa da yawan mutanen wurin nan za su ji daɗi, mutane nawa ne suka tuna da shantu? Duk muna da su, a kira su mana amma sai tsitsi da Fiyano.”

“Kuma ba ina wofantar da ‘yan fiyano ba ne, su ma suna da na su ta’adodin kuma na saurare su domin anan gurin akwai dattijuwa a nan vangaren, akwai kuma zafafan nigogi, waxannan zafafan nigogin su ma lokacin su zai zo.

“Amma idan muna so mu raya al’darmu to dole waɗannan zafafan nigogin su san cewa akwai ƙa’ida ta Bahaushe sannan waxannan kayan kiɗan na Bahaushe za a iya amfani da shi a wannan zamanin, akwai qasashe da yawa da suke irin haka. Irinsu Mali da Sanigal da Gambiya duk suna amfani da kayan kiɗan gargajiya, kuma suna koyi da yarensu na gargajiya akan qa’ida, har sun fito da wani kiɗa da ake cewa (World music) kixa ne da duk duniya ta san da muhimmancinsa”

Ya ce “A Nijar akwai Marigayi Mamman Barka, babu inda ba ya zuwa a ƙasar Turai saboda suna sha’awar su ga sun ga wannan kayan kiɗan na  gargajiya da ya ke amfani da su.

“Ba za ka je Ingila ko Faransa ko New York ka je da fiyano ka ce za ka burge Bature ba, ba za ta yiwu ba, amma idan ka ɗauki kalangu ka doka ka ce a ba ni lamba one da kalangu ka gani idan ba za ka yi daraja a gunsu ba”, inji Farfesa Abdullah.

Sannan ya qarqare da cewa, indai ana so a  burge shi to a zo masa da kalangu da sarewa da kukuma da gurmi, ba mamin za a yi ba a sanya waƙa a cikin kwamfiyuta ba, a zauna ana ta mamin ba.

An gabatar da maƙalu daban-daban da suka haɗa da cimakar Hausawa da magungunan Hausawa, da wasan langa da sauran su.

Taron ya samu halartar manyan Farfesoshi da daktoci da suka zo a ciki da wajen jami’ar da sauran al’ummar Hausawa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here