Suleiman Umar
@ katsina city news
Dan siyasar nan da sha takarar neman gwamna a baya Alhaji umar Tata ya bayyana ma jaridun katsina city news cewa ya fito a tsanake da kuma shirin shi don neman takarar gwamnan katsina a zaben 2023 mai zuwa in Allah ya kaimu.
A wata tattaunawa da babban editan jaridun yayi dashi ta waya daren talata 8/6/2021.Alhaji Umar Tata ya bayyana cewa ya bada takardar sa ta sanarwar kudurinsa na ajiye aiki a inda ya koma aiki a gwamnatin tarayya.
Kuma yanzu ya komo harkar siyasa da neman takarar gwamnan katsina gadan gadan a shekarar 2023 insha Allah.
Da aka tambaye shi wane matsayi yanzu yake a neman takarar tasa? Yace yanzu muna matakin ganawa da mutane da magana da dattawa da kuma duk wani abu da bai Saba ma dokar zabe ba.ko neman takara.
Yace wasu motoci da aka ga suna yawo a duk fadin jahar katsina, da yawan su masoyanshi ne.da wadansu da ya taba taimako yanzu suna da hali suke saye suna badawa a matsayin gudummuwa.
Umar Tata yace a wata mai kamawa zai wani shirin ganawa da jikokinshi na shiyyar Daura ,katsina, da funtua.
Yace ya ya na matan da ya taba aurar wa a lokacin da ya taba yin wani shiri aurar da Mata a shekarar 2015.
Yace zai gana da ya yan da aka Haifa karkashin wancan shirin kuma zai masu Alheri abin da Allah ya hore.
Umar Tata yace zai fito takarar shi ne a karkashin jam iyyar sa ta APC.
A baya Tata ya taba neman takarar gwamnan katsina a karkashin jam iyyar PDP da kuma jam iyyar APGA. yanzu kuma ya kuduri niyyar fitowa a jam iyyar APC a zaben 2023.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here