Na kasance cikakken dan jam’iyar APC a Najeriya tun sanda aka yanke mata cibiya shekaru kusan goma da suka wuce, wato tun watan February na shekarar 2013.

Ina cikin wadanda suka zaga kasar nan domin yin tallan jam’iyar ta APC sanda aka kafa ta, tun daga matakain mazabu, zuwa jiha da kasa baki daya. Na sadaukar da rayuwa ta tare da mika wuya na kacokan, wajen gina jam’iyar, da zummar cewa zamu kawo sabon sauyi a kasar nan, tare da fiddo da miliyoyin yan Najeriya daga cikin mawuyacin halin da muke ciki, na kuncin rayuwa, da samar da yalwatar arziki da aikin yi da tsaro da sauran su.

A shekarar 2019, haka muka sake fita neman kuri’a ganin cewa watakila shekaru hudu sunyi kadan a iya wani abin kirki ganin yadda al’amuran suka lalace matuka, dan haka muka sake neman mutane su zabi gwamnatin mu ta APC, wanda aka lashe zaben a karo na biyu. Sai dai abin takaicin shine a zaben farko da na biyun, duk kwalliya bata biya kudin sabulu ba, da gwamnatin da jam’iyar duk sake tabarbarewa al’amuran su, su kayi.

Ita gazawa bata da uba, kowa gudun ta yake. Zaka ga ba wanda yake so a ce ya gaza, koda kuwa hakan ne. Amma ita APC, masu mulkin ta basu ma yarda cewa sun gaza ba, hasali ma gani suke ba’a taba gwamnati da tayi aiki kamar ta su ba. Kullum sai dai kaji suna koda kan su, suna ta yabon kan su, suna ganin sun fi kowa aiki. Amma abin takaicin shine yadda basu ma san halin da talaka yake ciki ba a kasar nan, kudin komai ya tsefe a kasar nan, wani abin ma da kudin ka baza ka samu ba. Harkar tsaro ta tabarbare, dan an kashe mutun dari a arewa a rana daya ba wani abin mamaki bane, har ya daina razana mutane. Komai ya lalace a kasar nan.

Hausawa suka ce ido mudu ne, Allah cikin ikon Sa Ya ba ni damar aiki a cikin gwamnatin jihar Kano na shekaru biyar karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, a karin farko na rike mukamin Director General Media sannan daga bisani na koma mai bawa Gwamna Shawara wato Special Adviser. Alhamdulilah bisa shaidar da mutane da yawa suka bayar, zan iya cewa nayi bakin kokari na wajen tallata aiyukan Gwamnatin jiha da kuma jihar ita kan ta. Aiki na na wayar da kai ne akan aiyukan da gwamnatin jiha take yi, wanda nayi bakin kokari na.

A cikin aiki na, na hadu da hadari kala kala, a zahiri da kuma na shafukan sada zumunta, na kuma san irin yadda Gwamnatin taraiya ta gaza wajen cika alkawarin da muka dauko a kasar nan, wanda gaskiya yake sosa min rai ba kadan ba.

Tun da na shiga siyasa shekaru ashirin da biyu da suka wuce, ina iyakar kokari na na kamanta gaskiya. Wanda suka san tarihin siyasa ta zasu tabbatar da haka. Wannan ce ta sa lokacin mulkin PDP muka soki gwamnatin su bisa yadda suke mulkin su. Toh amma idan na soke su saboda gazawar su, kenan ya zama wajibi na soki APC ita ma tunda ta gaza, idan dai za’ai adalci. Na yi iyakar kokari na domin na ga an gyara abubuwan nan tun daga cikin jam’iyar da ma ita kan ta gwamnatin, har ta kai ta kawo ina fada a baiyane duniya ta gani. Wannan ta jawo aka dakatar da ni daga aiki a watan October na shekarar 2020, sannan daga bisani jami’an tsaro suka kama ni suka tsare, sannan aka sallame ni daga aiki a watan February na shekarar 2021, saboda na ce gwamnatin taraiya ta gaza akan matsalar tsaro.

Toh bisa wadannan dalilai, ya sa naga ya dace na tsaya akan ra’ayi na ba tare da an tauye min shi ba, haka kuma nayi shawarwari da yan’uwa na na kusa da abokan arziki da yan siyasa da muke tafiya tare, na yanke hukuncin na hakura da jam’iyar APC, na kuma fice daga cikin ta a yau, ranar litinin ashirin ga watan March.

Zan ci gaba da tuntubar na gaba da ni, da sauran abokan tafiya ta na siyasa, domin yanke shawarar matakin gaba da zan dauka nan ba da dadewa ba a siyasance.

Bazan karkare rubutun nan ba, sai na mika godiya ta ta musamman ga Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR bisa damar da ya bani, na bada gudunmawa ta wajen gina jihar Kano har tsahon shekaru biyar. Wannan abune da har abadah bazan manta da shi ba a tarihi na, koda bama tare a siyasance, zan ci gaba da girmama shi a matsayin Uba, saboda damar da ya bani. Allah saka da alheri.

Daga karshe, wadanda suka sanni musamman a shafin twitter, sun san take na shine #ZeroTension, wato babu fargaba ko damuwa. Dan haka ina nan akan wannan take na #ZeroTension, saboda a cikin Suratul Tawbah aya ta hamsin da daya, Allah Ya na cewa:
Ka ce: “Babu abin da yake samun mu face abin da Allah Ya rubuta saboda mu. Shi ne Majibincin mu. Kuma ga Allah, sai muminai su dogara.”

Nagode Allah tabbatar mana da alherin Sa a duk inda muke! Amin.

Salihu Tanko Yakasai (Dawisun Kano)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here