Na fi son Messi ya yi ritaya a Barcelona – Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ya fi son Lionel Messi ya kammala rayuwarsa ta ƙwallon kafa a Barcelona.
Guardiola ya tsawaita kwangilarsa da Manchester City inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a ranar Alhamis, kuma nan take aka alaƙanta da shi da tsohon ɗan wasansa wanda saura kaɗan ya dawo ƙarƙashinsa.
A ƙarshen bazara kwangilar Messi za ta kawo ƙarshe kuma yana iya ƙulla yarjejeniyar da duk wata ƙungiya a wajen Spain daga watan Janairu.
Guardiola ya ce: ” Messi ɗan wasan Barcelona ne. Na fada ba sau ɗaya ba. a matsayi na masoyi, ina son Leo ya ƙare rayuwarsa a can”
A watan Agusta Messi ya so barin Barcelona, kuma lokacin an yi tunanin zai koma Man City kafin shugaban Barcelona ya hana shi tafiya.