Daga Muhsin Tasi’u Ya’u, Kano
A yau litinin 9-5-2022 ne wasu kungiyoyi guda dari da biyar karqashin jagorancin HASSAN GARBA SOLIDARITY,MOVEMENT TANKA 2023, tare da dubban al’umma daga ko wanne sassa na karamar hukumar Kumbotso Suka gudanar da wani gangamin taro a saketeriyar mulki ta karamar hukumar Kumbotso da ke cikin birnin jahar Kano. Bayan zaman dako da al’ummar wannan karamar hukuma suka yi, wanda ya kama da matasa, mata tareda dattijai kuma gogaggun yan siyasa, daga kan mazabu guda goma sha daya tare da kansilolin su, shugabannin jam’iyya da sauran su. sukai cikar kwari a cikin wannan karamar hukuma, inda suke sa ran shigowar mai Girma ciyman na wannan qaramar hukuma ta Kumbotso, inda matasa, dalibai da mata suka dunga daga allo da rubutun cewa dole sai ya fito wannan takara ta majalisar tarayya, domin wasu dalilai. Inda suka dinga ikararin shi kadai ne shugaban karamar hukumar da a cikin shekara daya yayi ayyuka da sun kai sama da dari da talatin, sannan ya bada jari da ababan more rayuwa har sau hudu duk a shekara daya, banda ayyukan raya kasa bila adadin. Taron ya samu halartar dattawa kuma jiga-jigai a wannan qaramar hukuma, sannan da ‘yan gwagwarmaya daga lungu da saqo na wannan qaramar hukumar, inda a tare da shi akwai dan uwan sa shugaban qaramar hukumar Tarauni Hon Habu P A, inda shi ma ya amince da wannan qudurin sannan yana goyon baya wannan tafiya dari bisa dari.
Haka zalika, shi ma mai gayya mai aiki Honorabul Hassan Garbann Kauye Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso mai ci, ya yaba da wannan tarba da akai masa da bUKatar da aka zo masa da ita. Inda ya bayyana cewa “da bamu yi abun kirki ba, da ba za a zo da wannan buKatar ba. Ganin cewa tun da aka kafa damokoradiyya ni ne mutum daya tilo a wannan qaramar hukuma da aka yiwa tayin na fito takara bayan ina kan kujerar mulki’’ daga qarshe da a’ulumma suka matsa sai ya furta da bakin sa, sai yace to Allah yasa hakan ya zamo Alkhairi gare shi dama Alummar karamar hukumar Kumbotso baki daya.
Shima a jawabin mai girma kansilan Mariri kuma shugaban masu rinjaye na majalisar zartarwa na karamar hukumar Kumbotso Hon Roja Mariri yace: “Wannan ijtihadi da muka fito domin fitar da al’ummar Kumbotso daga kangin mulkin bauta da ake musu ya zo karshe, wannan dalili ya sa suka ga cewa ba wanda ya dace da wannan kujera kamar Hon Hassan Garba. Duba da dubban ayyuka da ya gabatar a qasa da shekara xaya a office” Sannan ya qara da cewa, kuma duka kansilolin wannan karamar hukuma guda goma sha daya duk sun tsaya a wannan matakin.
Daga karshe shi ma mataimakin shugaban majalisar zartarwa na wannan karamar hukumar kansilan Fanshekar Hon Ma’aruf Zawaciki ya ce wannan aikin alherin da suke son su yi wa al’ummar wannan karamar hukumar ba gudu ba ja da baya kuma yana fatan samun nasara. Sannan ya yi kira ga mai girma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da shugaban jam’iyya dan sarki Hon Abudullahi Abbas cewa lallai wannan kuduri nasu ya kama ta a kalle shi da idon basira kuma daman shi mai girma gwamna aiki yake so ayi wa Al’umma, kuma ga ma’aikaci an samu. Sannan yai addu’ar fatan samun nasara da kuma Allah ya maida kowa gida lafiya Ameen.