Kungiyar nakasassu a Jamhuriyar Nijar ta gudanar taron addu’o’i don neman zaman Lafiya yayin zaben da za a yi na shugaban kasa da na ‘yan majalisa.
An gudanar da taron addu’o’i ne a babban Masallacin Juma’a dake birnin Yamai, da hantsi inda daruruwan mutane masu nakasa suka hallara domin gudanar da addo’in zaman lafiya.
A lokacin da kasar ta shiga yanayin da ake cigaba da jiran sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 13 ga watan Disamba, wanda ke dai-dai da lokaci da ya rage kwanaki 10 a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da na shugaban kasa.
Shugaban kungiyar addinin Islama ta AIN Cheik Djibril Soumaila Karanta shine ya jaogranci wadanan addu’oi.
VOAHAUSA