Suleiman Chiroma @Katsina City News

Wanda zai jagoranci shirya kongress na jam’iyyar APC a Jihar Katsina sunansa Alhaji Muntari Lawal, yana da sarautar Madugun Katsina.

Shi ne Shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Katsina.

An haife shi a 2 ga watan Fabrairu, 1951. Ya fito daga zuriyar malanta da kasuwanci.

Ya yi karatu a Barewa College Zariya. Daga nan ya wuce makarantar share shiga Jami’ar da ake kira KCAST.

Daga nan ya tafi zuwa kasar Faransa, inda ya yi digiri na farko da na biyu a kan dangantakar kasashe da kuma Kimiyyar Siyasa.

Ya dawo gida Nijeriya a 1978, inda ya yi hidimar kasa (NYSC) a Jami’ar Bayero ta Kano a Tsangaya Nazarin Ilimin Kimiyyar Siyasa.

Yana gama hidimar kasa ya kama aiki da tsohuwar Jihar Kaduna a matsayin babban mataimakin Sakatare a ofishin Gwamnan Jihar Kaduna.

Ya fara siyasa a 1979, inda ya shiga jam’iyyar canji da ake kira PRP. Bayan an ci zabe aka ba shi mukamin mai ba Gwamna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa shawara a kan harkokin siyasa.

Ya rike matsayin mai ba Gwamnan Katsina shawara a zamanin Alhaji Umaru Musa ‘Yar’adua a zangon farko da na biyu. Sai karshen zango na biyu ya koma goyon bayan takarar Aminu Bello Masari.

Tun a lokacin bai canza ba. Duk shekaru takwas da Gwamnan Katsina Shema ya yi a mulki ba ruwansa, yana gida bai tsoma baki ko katsalandan a cikin gwamnatinsa ba. Bai kuma yi maula, bambadanci ko bara ba.

Har aka manta da shi. Sunansa ya kara fitowa a zaben 2015. Bayan an ci zabe sai aka ba shi Babban Sakatare, kuma mai ba da shawara a gidan gwamnatin Katsina.
Yana cikin shugabannin kamfen din APC na 2015 da 2019

Ya yi Amirul Hajj a 2019, inda ya ba marar da kunya. A lokacinsa aka yi wa Hukumar Alhazai gyaran fuskar da har yanzu ake alfahari da shi.

Daga cikin ayyukan da Alhaji Muntari Lawal ya yi, har da koyarwa a manyan makarantun gaba da sakandare. Ya yi aikin gwamnati har a Karamar Hukuma.

Yana jin Turanci, Faransaci, Hausa da kuma Larabci.

Muntari Lawal mutum ne mai akida da tsayawa a kan gaskiya.

Yana matsayin mai ba Gwamna shawara a zamanin Umaru Musa ‘Yar’adua ya balle ya goyi bayan takarar Aminu Bello Masari a 2006.

Zaben shi a matsayin wanda zai jagoranci shirya babban taro na APC a Katsina ya sanya duk ‘yan jam’iyyar hankalinsu ya kwanta.
‘Yan kwamitin da zai yi aiki tare da su ba za su iya juya shi ya yi rashin gaskiya ba.

Daga Abuja ko a Katsina, ba wanda ya isa ya yi masa kiran mai tallar taba.

Za a fara kongress na APC daga unguwani a ranar 24 ga watan Yuli.

Katsina City News
Www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
Www.thelinksnews.com
07043777779 081 37777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here