Mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, ya yi shekaru 67 babu wanka

Wannan mutumin da kuke gani sunanshi Amou Haji tsoho ne mai shekaru 87 wanda ya kwashe shekaru 67 bai yi wanka ba, Tabbas hakan yake.

Tsohon dan asalin kasar Iran yana rayuwarsa ne kusa da wani kauye dake kusa da yankin Kermanshah shi kadai kuma ya yi a kalla shekaru 67 babu wanka.

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar,, Haji a kodayaushe za ka gan shi lullube da toka da datti kuma bayan wanka saboda tsoron ruwa da yake yi.

Tsohon mai shekaru 87 ya yadda cewa idan har yayi wanka, toh babu shakka zai iya faduwa mugun ciwo.

Abincin da tsohon yake ci sun hada da rubabben nama da matattun dabbobi. Yana matukar jin dadin cin bushiya da shan tabarsa ta koko, India Times ta ruwaito hakan.

A wasu lokutan kuwa, Haji yana busa hayakin kashin dabbobi a kokon tabarsa.

Killataccen tsohon ya yanke shawarar irin wannan sabuwar rayuwar ne bayan da ya samu wani babban kalubale a zamanin samartakarsa.

Duk da tsohon bai yarda da yin wanka da ruwa ba, an gano cewa yana shan a kalla lita biyar ta ruwa a kowacce rana daga wani gwangwaninsa mai tsatsa, Times Now News ta ruwaito.

Yana gyara gashin kansa ne tare da rage masa tsawo ta hanyar kona shi da wuta.

Legit NG

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here