Mutumin da ke son korar Fulani daga jihohin Yarabawa ya shiga Ogun

Sunday Igboho

Mutumin nan da ya bai wa Fulani makiyaya wa’adin ficewa daga jihohin Yarabawa mai suna Sunday Igboho ya je Jihar Ogun domin korar Fulanin da ke zaune a Jihar.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce ba ita ta gayyace shi ba, yayin da yake zagaye a jihohin Yarabawa na yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Ogun, Abdulwaheed Odusile, shi ne ya yi watsi da rahotannin gayyatar tasa cikin wata sanarwa a Abeokuta, babban birnin jihar.

Ya ce an ruwaito kalaman da Remmy Hazzan, wani mai taimaka wa gwamna kan kafafen yaɗa labarai, ba daidai ba waɗanda ya yi a cikin wata hira da wata kafar yaɗa labarai.

“Sun gurɓata kalaman nasa ne domin tayar da hargitsi,” in ji shi.

Sunday Adeyemo ya yi wa matasa jawabi a Ogun a jiya Litinin, inda ya shiga daji domin zaƙulo Fulanin da ke zaune a jihar.

A makon da ya gabata ne ya bai wa Fulani wa’adin kwana bakwai su fice daga Jihar Oyo sakamakon zarginsu da yin garkuwa da mutane da fyaɗe da kuma kisan manoma a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here