Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce jumillar mutum 69 ne suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar EndSars da ta rikiɗe zuwa rikici a ƙasar.
Buhari ya faɗi hakan ne yayin ganawar da ya yi da tsofaffin shugabannin Najeriya da hafsoshin tsaro a yau Juma’a a fadarsa ta Aso Villa.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai fararen hula 51 da ‘yan sanda 11 da sojoji bakwai.