Mutum 300 Sun Amfana Da Tallafin Zakka A Gonar Dadin Kowa

A karshe makon da ya gabata ne hajiya zainab Garba Danammani Funtua wacce aka fi sani da gimbiya ta gudanar da zakkan kayayyakin masarufi a babbar gonar ta da ke kauyen Dakamawa a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina, zakkan dai an gudanar dashi ne ga talakawan wannan kauye da gajiyayyu a yayin da mabukata kimanin 300 su ka amfana.
ita wannan zakka dai an saba aiwatar da ita ne a duk shekara tsawon shekaru da dama da suka shude a wannan gona ta mai martabiya da ke kauyen Dakamawa a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.
kayayyakin masarufin da aka raba a wannan karon sun hada da buhunnan gero, dawa, garin masara, taki domin amfanin manoma, sai kayan itatuwa ga talakawa mabukata akalla 300.
a lokaci guda kuma Gimbiyar ta kaddamar da ginin da ta ke aiwatar wa domin ajiye kayayyakin amfanin gona da takardu mallakin ta inda ta rada ma wannan wuri suna ‘Baba Buhari excellent central administration’, ta sa ma wannan wuri sunan shugaban kasa Muhammad Buhari ne sakamakon duba da yadda shugaban ya bawa manoma muhimmanci da kuma irin gudammuwa da rawar ganin da ya ke takawa a harkan noma.
ita dai wannan gona ta mai martabiya mai suna ‘Gonar Dadin Kowa’ ta marigayi Garba Danammani Funtua ta samo asali ne daga mahaifin mai martabiya wanda aka fi sani da Garba Danammani Funtua da ke kauyen Dakamawa a karamar hukumar Funtua, Marigayi Garba Danammani dai shahararren manomi ne wanda kowa ya shaida babu manomi kamar sa a duk fadin garin Funtua, sannan an shaide shi wajen bayar da tallafin kayan masarufi a duk shekara ga talakawan garin wanda aka fi sani da zakka a musamman wajen gabatowar watan ramadana wato watan azumi.
hakan ya sa Gimbiya ta dage wajen ganin ta tafi akan wannan turba na mahaifin nata na bayar da zakka a duk shekara.
Gimbiyar dai ta na raba amfanin gonar nata ne kashi uku a duk irin wannan lokaci, kashi daya ta bayar da zakka, kashi daya kuma ta rabawa ma’aikatan wannan gona nata, sannan kashi daya kuma ta yi amfanin kanta da shi.
sannan a karshe kuma Gimbiyar ta yi kira ga manoman Nijeriya da su kara kaimi wajen taimakon al’umma musamman a irin wannan lokaci da zamu shiga na watan ramadana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here