Mutum 12 sun mutu kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Copyright: Samuel Aruwan
Mutum 12 sun mutu, 25 sun samu raunuka sakamakon wani haɗarin mota da ya faru kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.
Kwamishinan ya ce cikin abubuwan da suka jawo haɗarin har da rashin kyawun hanya da tuƙin ganganci da kuma gudu da mota.
Ko a farkon watan Disamba sai da mutum 16 suka mutu sakamakon haɗarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zaria.
